Kotu ta tsare wani magidanci kan laifin tarawa da matarsa ta dubura a Kano

Kotu ta tsare wani magidanci kan laifin tarawa da matarsa ta dubura a Kano

Wata kotun Majistare dake Kano a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, ta bada umurnin rufe wani magidanci dan shekara 30 mai suna Balarabe Salisu, wanda ake zargi da yin ma’amalar auratayya da matarsa yar shekara 20 ta dubura.

Rundunar yan sanda na tuhumar Salisu Wanda ya kasance kurma da laifin saba ma hanyar Mahallici.

Mai shari’a a kotun, Muhammad Jibril, yayi umurni ga yan sanda da su mayar da fayil din karan zuwa ga daraktan hukunta jama’a don jin shawarar sa.

Jibril ya daga karan zuwa ranar 10 ga watan Yuli don cigaba da sauraron karan.

A baya, mai gabatar da kara, Inspekta Pogu Lale, ya sanar da kotun cewa Mallam Abubakar Umar dake Dorayi Karama Quarters a Kano ya kai karan a ofishin yan sanda reshen Dorayi Babba Kano a ranar 14 ga watan Yuni.

Lale ya fada ma kotun cewa mai laifin ya auri diyarsa wacce ta kasance kurma a watan Maris 2019.

Yayi zargin cewa mai laifin a lokuta daban daban ya sadu da diyarsa ta dubura.

KU KARANTA KUMA: Kuji abin al'ajabi: Wasu tagwaye sun mutu a daidai ranar da aka haifesu, kuma cikin irin yanayin da aka haifesu

Yace, laifin ya saba ma sashi na 284 na tsarin dokoki.

Bayan an karanto mishi laifuffukansa, bai amince da aikata laifin ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel