Sojoji sun hallaka yan bindiga 24 a Kaduna, Kano da Neja

Sojoji sun hallaka yan bindiga 24 a Kaduna, Kano da Neja

Rundunar sojin atisayen Operation Harbin Kunama na jihar Kaduna sun hallaka akalla yan bindiga 24 a jihohin Kaduna, Kano da Neja kuma sun damke 61.

Kwamandan Janar na yankin Division 1, Manjo Janar Faruk Yahya ya bayyana hakan ne a wani hira da manema labarai da ya gudana ranar Laraba, 26 ga Yuni 2019 a hedkwatan hukumar dake jihar Kaduna.

Game da cewarsa, an ceto mutanen da aka sace 20 daga sassan masu garkuwa da mutane kuma sun mayar da su wajen iyalansu.

A jawabinsa, ya yi bayanin cewa yawan sace-sacen mutane, barandaci, dabanci, da ya addabi arewacin Najeriya musamman arewa maso yammaci ya sabbaba kafa atisayen Operation Harbin Kunama da babban hafsan soji, Laftanan Janar Tukur Buratai yayi ranar 1 ga Afrilu, 2019.

Amma ya bukaci al'ummar gari su taimakawa jami'an tsaro da bayanai a kan lokaci ba sai an gama kai hari ba.

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta ceto yan kasar Lebanon uku da aka sace a jihar Rivers

A bangare guda, Dakarun Soji na 120 Task Force Battalion da ke Goniri a jihar Yobe sunyi nasara kashe 'yan ta'adda masu yawa a wani harin kwanton bauna da suka kai musu misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.

Sojojin sun kafa tarko ne inda suka jira 'yan ta'addan suka matso kusa sannan suka yi musu luguden wuta a yayin da suka taho a motoccinsu masu dauke da bindigu guda bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng