Allah daya gari banban: Garin da ake daukar kunkuru kamar gwal

Allah daya gari banban: Garin da ake daukar kunkuru kamar gwal

Hukumar kasar Malaysia sun kama kunkuru har guda 5,000 a cikin wata jaka a filin jirgin sama na Kuala Lumpur, inda nan take suka karbe su.

An damke wasu mutanen kasar Indiya guda biyu bayan an gano tarin kunkurun - masu jan kunne kuma wadanda ke iya rayuwa a waje da kuma cikin ruwa a cikin wasu kwanduna kunshe a cikin jakunkunansu.

Mahukuntan sun ce yawan kunkurun ya kai na kimanin dala $12,700, kuma an yi yunkurin safararsu ne zuwa kasar Indiya.

Malaysia ta zama matattarar masu safarar dabbobi wadanda ake kai su kasashen Asiya.

An cafke mutane biyun ne a makon da ya gabata bayan sun isa Kuala Lumpur daga birnin Guangzhou na kasar Sin, kamar yadda babban jami'in hukumar kwastam Zulkurnain Mohamed Yusof ya bayyana, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Mutanan masu shekaru 30 zuwa 42 ba su da izinin mallakar kunkurun, in ji shi, kuma yanzu za su iya fuskantar daurin shekara biyar a gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Malabu: Tsohon Jakadan Rasha, Ednan Agaev, ya bayyana a gaban kotun Italiya

"Wannan shine karo na farko da muke ganin irin wannan laifin, sannan kuma ba za mu iya tabbatarwa ko ya kai girman abin da muka saba gani ba.

"Sai dai da alama kunkurun na da yawa ganin yadda aka same su cikin akwati biyu a lokaci guda," cewar Mista Yusof ga taron manema labarai a ranar Laraba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng