Yaqi tsakanin Amurka da Iran ba zai dau tsawon lokaci ana yin sa ba – Trump

Yaqi tsakanin Amurka da Iran ba zai dau tsawon lokaci ana yin sa ba – Trump

-Kalaman Donald Trump na nuna cewa akwai alamr za'a gwabza yaqi tsakanin Amurka da Iran

-Shugaba Donald Trump ya ce ba wai yana da sha'awar yin yaqi da kasar ta Iran bane, amma idan har ya kama za suyi yaqin ba za'a dade ana yinsa ba

A ranar Laraba, Shugaba Donald Trump ya ce, ba wai yana sha’awar yakar kasar Iran bane, amma idan har ta kama sai an gwabza yaqi a tsakaninsu to ba ko zai dau tsawon lokaci ana yinsa ba.

Trump yayi tsokaci a kan cewa, idan har za’a gwabza yaqin, jiragen sama ne kawai za su rika kaiwa da komowa. A don haka babu buqatar sai an tura dakaru zuwa can kasar.

KU KARANTA:Rashin lafiyar Zakzaky da matarsa ya yi tsanani – IMN

Jawabinsa ya biyo bayan zancen Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, inda yake kokarin yayyafawa wutar dake tsakanin kasashen biyu ruwa , ta hanyar cewa “ Iran ba yaqi take nema da Amurka ba.”

Kasar Amurka ta riga da ta qaqabawa Iran takunkumin tattalin arziki, tun bayan da Iran ta harbo jirgin saman kasar maras matuki a yankin Gulf a makon da ya gabata.

A wata tattaunawa da Trump yayi da tashar Fox Business News, inda aka tambayesa shin Amurka zata gwabza yaqi da Iran ?.

Ga abinda Shugaban ya ce: “ To, bana fatar hakan dai a yanzu, amma dai muna nan cikin shiri don gudun abinda kan iya zuwa ya dawo. Ko da a ce yaqi ya kaure, ba zai kwashi lokaci mai tsawo ba. Bamu da buqatar sai mun tura dakaru domin yaqar Iran. Abinda kawai zan fadi shi ne, idan suka sake yin wani kuskure guda to haqiqa za su ga fushin Amurka.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng