Wuta Wuta: Sojoji sun ba yan ta’addan Zamfara sa’a 24
-Kwamandan yaki da yan Ta'adda na jihar Zamfara ya ba yan ta'addan sa'a 24 su mika wuya ko kuma ya shafe su daga doran kasa
-Kwamanda ya bayyana bacin ransa cewa yan ta'adda sun cigaba da kai hari duk da cewa gwamnan yayi alkawarin zai yi afuwa ga duk wanda ya mika wuya
-Ya bayyana cewa tun da yan ta'addan basu shirya yin sulhu ba, zai bisu har mafakarsu ya gama dasu
Kwamanda na Operation Hadarin Daji, Maj- Gen Jide Ogunlade, a ranar Talata ya ba yan ta’adda wa’adin sa’a 24 a Zamfara, da su mika wuya ko kuma suga “yakin da ba a taba yin irinshi ba.”
Ogunlade yayi gargadin a wani taron yan jarida da aka gudanar a hedikwatar sojoji da ke Zamfara.
Ya bayyana bacin ransa akan yadda yan ta’adda suka ki mika wuya su daina ta’addancin a cikin watan Mayu bayan da gwamnan jihar, Alhaji Bello Matawalle ya ce zai yi afuwa ga duk wanda ya mika wuya.
KARANTA WANNAN: Kada ka sake jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki - PDP ta gargadi Buhari
Kwamandan ya ce “Abun takaici ne ace cikin yan sa’o’i bayan da gwamna ya ce zaiyi afuwa, aka kai hari 20 a kauyuka daban daban.
“Wannan ya nuna cewa yan ta’addan basu shirya yin sulhu ba; shi yasanya yanzu zan basu sa’a 24.
“Yanzu hanya daya da ta rage masu shine su mika wuya, su aje makamansu, ko kuma su yi kuka da kansu.” A cewarshi.
Kwamandan hukumar, ya ce yan ta’addan na yin amfani da ganin cewa sojoji na bin ka’ida shi ya sanya suke boyewa cikin jam’ar gari a duk sanda sojoji ke bin su. Yayi gargadi cewa “wannan karon, za muje har mafakarsu inda za’ayi tabargaza mu fatattake su.”
“Ina so in ba jama’ar jihar nan tabbaci cewa ta’addanci ya kusa zama tarihi a Zamfara bayan wannan yakin da zamu yi nan da sa’a 24.
“Za mu tabbata cewa manoma sun cigaba da aikin nomansu kuma yan gudun hijira zamu koma gida cikin lumana.”
Kwamandan ya godewa gwamnatin tarayya da ta samar da aikin Operation Hadarin Daji ya kuma yabi shugaba Muhammadu Buhari akan tallafin da yake basu.
Yan jarida sun ruwaito cewa Operation Hadarin Daji an kaddamar da shi a ranar 10 ga watan mayu 2019 wanda aka ta’allaka shi ga jihar Zamfara kadai, wanda ya canji Operation Sharan Daji.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng