Kuma dai: Rikici ya sake barkewa a jihar Taraba, an hallaka 1, an kona gidaje

Kuma dai: Rikici ya sake barkewa a jihar Taraba, an hallaka 1, an kona gidaje

- Rikicin kabilun Jukun da Tibi ya ki ci ya ki cinyewa

- Gwamnonin Benuwe da Taraba sun kasa kawo karshen kashe-kashe

- An yi asarar rayuka dabiliyoyin dukiyoyi kawo yanzu

Akalla mutun daya sun rasa rayukansu ranar Takata kuma an gona gidaje da dama a sabon rikicin da ya barke tsakanin yan kabilar Jukun da Tibi a kauyen Rafinkada dake karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.

Shugaban kwamitin rikon kwarya, Daniel Adidas, ya tabbatar da wannan labari a hirar wayar tarhi da kamfanin dillancin labarai a Jalingo.

Mista Daniel Adidas ya bayyana cewa wasu mutane sanye da rigunan sojoji suka afka Rafinkada suna kona gidaje.

Shugaban karamar hukumar ya ce jami'in soja daya ya samu rauni kuma yana jnya a wani asibiti a garin Wukari.

Ya kara da cewa kuran ya kwanta yanzu bayan tura dakarun sojoji.

KARANTA: Abubuwa 5 da kungiyar Yarbawa ta roki Shugaba Buhari

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP David Missal, ya tabbatar da rahoton amma ya ce mutum daya kadai aka kashe.

Yace: "Rahoton da nake dashi na nuna cewa wasu yan bindiga daga jihar Benue sun kai hari karamar hukumar Wukari inda suka kashe mutum daya da kona gidaje."

Za ku tuna cewa rikici tsakanin kabilar Tibi da Jukun ya sabbab hallakan rayuka da dama da asarar dukiyoyi musamman a kauyukan da ke tsakanin jihar Benuwe da Taraba sun watan Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng