Chelsea za ta bawa wani tsohon dan wasanta aikin koci
- Akwai yiwuwar tsohon dan wasan kwallon Chelsea, Frank Lampard zai koma kungiyar amma a matsayin koci
- A halinyanzu an bawa kungiyar Chelsea damar tattaunawa da Derby County kan batun zawarcin Lampard a matsayin kocin ta
- Idan cinikin ta yiwu, ana sa ran Lampard zai maye gurbin Maurizo Sarri wanda ya bar Chelsea ya koma Juventus
An bawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila damar tattaunawa da kungiyar Derby County, kan batun zawarcin Frank Lampard a matsayin kocinta.
Lampard mai shekaru 41 ya yi shekaru 13 a kungiyar Chelsea a matsayin dan wasa kuma ana sa ran zan maye gurbin Maurizo Sarri wanda ya koma kungiyar Juventus a bana.
Kungiyar Chelsea za ta biya kungiyar Derby fam miliyan hudu idan ta dauki Lampard a matsayin kocinta.
Lampard ya fara aiki a matsayin kocin Derby ne a 2018 inda ya yi nasarar kai kungiyar wasannin cike gurbin shiga gasar Premier amma su ka sha kaye wurin Aston Villa a wasan karshe.
Tsohon dan wasan tsakiyar na kungiyar Chelsea ya buga wasanni 648 inda ya lashe manyan kofi guda 11.
Derby ta ce duk da cewa suna shirin tunkarar kakar wasa ta 2019, dukkan kungiyoyin na fatan cimma matsaya nan ba da dewa ba.
Kazalika, Derby ta ce ba za ta kara cewa komi kan lamarin ba har sai bukatar hakan ta taso.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng