Dalilai 7 da ke sa matasa kashe kansu

Dalilai 7 da ke sa matasa kashe kansu

A yan kwanakin bayan nan ana ta samun karuwar yawan matasa da ke hallaka kansu da kansu, wannan al’amai ya janyo hankalin masana inda suka yi kira ga cewar ya kamata tun wuri ayi wa tufkar hanci.

Wata hanyar da matasan ke amfani da ita wajen kashe kansu ita ce amfani da maganin kwari da ake kira 'Sniper'.

Sakamakon haka ne a makon da ya gabata a gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta yin maganin kwarin a kasar da manufar dakile yawaitar kisan kai.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci ta Najeriya (NAFDAC), ta ce tana son ganin an sauya kwalbar maganin kwarin ko hakan zai hana matasa shan sa.

Masu nazarin zamantakewar dan adam irin su Farfesa Sadiq Radda na Jami'ar Bayero ta Kano ya zayyana dalilai guda bakwai da ya ce su ne suke jefa matasa halin kashe kai:

1. Kuncin Rayuwa

Yawan bakin ciki da kunci rayuwa na daya daga cikin abunda ke tunzura matasa harma suka cewa daukar ransu shine mafita da zai rage asu radadin abunda suke ji.

2. Matsin iyaye

Wasu lokutan matsi da takurar iyayena daga cikin abubuwan da ke sanya matasa hallaka kansu. Misali a kan harkar aure, wasu iyayen da zaran yaransu sun kai minzalin aure kuma babu manemi sai su fara uzura masu.

KU KARANTA KUMA:

3. Takurawar abokai

Matsin abokai na daya daga ckin abubuwan da ke haddasa matasa kashe kansu a wannan zamani.

4. Takurarwar makwabta

5. Fina-finai

Wasu lokutan abubuwan da mutane ke kallo a fina-finai kan zamo masu abun dagora wajen kamanta abunda suka gani musamman idan halin dasuke ciki yayidaidai da wanda ke kunshe a fina-finan.

6. Kafofin sa da zumunta na zamani

Kafofin zumunta na zamani na taka muhimmin rawa a halin da matasa ke ciki a yanzu

7. Rashin hakurin matasa kan rayuwa

Gajen hakuri da gaggawa yayi wa matasan wannan zamani yawa, ta yadda basa daukar dangana da kaddara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel