Kwamandan Soji ya tona asirin su waye a cikin 'yan bindigan Zamfara

Kwamandan Soji ya tona asirin su waye a cikin 'yan bindigan Zamfara

Kwamandan Operation Hadarin Daji ya ce akwai 'yan bindiga da 'yan ta'adda a cikin wanda ke kai hare-hare a jihar Zamfara.

Kwamandan Manjo Janar Jide Ogunlade ya bayar sanarwar ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a hedkwatan rundunar da ke Gusau a ranar Talata.

"A yanzu fa 'yan ta'adda da 'yan bindiga sun yi kutse cikin kungiyoyin maharan da ke kai hare-hare a Zamfara.

"'Yan bindiga yanzu sun fara rikidewa suna komawa 'yan ta'adda saboda ko a rawaninsu akwai rubutu na 'Jihadi'.

DUBA WANNAN: Jerin kasashe biyar da rabin masu fama da matsanancin talauci a duniya ke rayuwa - Rahoto

"Tunda bata garin suna canja dabarunsu, ya zama dole mu canja namu. Idan adadin su na karuwa, za mu bawa gwamnatin tarayya shawara ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda," inji shi.

Ya cigaba da cewa "Dakarun mu suna cike da izza saboda irin gudunmawar da fadar shugaban kasa da shugabanin sojoji ke bawa Operation Hadarin Daji.

"Ina tabbatarwa 'yan Najeriya cewa dukkan dakarun mu da jami'an mu suna gudanar da ayyukansu kan yadda doka ta tanada musamman wurin tabbatar da cewa ba a taba farar hula ila wurin kai hare-hare.

"Mun bude sashin sauraron koken al'umma da ke bude sa'o'i 24 saboda mutane su rika kira suna bamu bayyanai masu amfani don kare tabbarbarewar tsaro.

"Muna fatar kamfanonin sadarwa za su bari al'umma su rika kiran mu a wannan layukkan ba tare da biyan kudin kira ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164