Dankari: Tsohon gwamnan jihar Ogun ya fito da bindigogi kirar AK47 guda 1000 da ya boye

Dankari: Tsohon gwamnan jihar Ogun ya fito da bindigogi kirar AK47 guda 1000 da ya boye

Gab da karewar wa'adinsa matsayin gwamnan jihar Osun, Ibikunle Amosun, ya tuntubi kwamishanan yan sandan jihar, Bashir Makama, domin bayyana masa cewa yana da dubunnan bindigogi da miliyoyin harsasai da ya boye a gidan gwamnati.

Ya kira kwamishanan yan sandan ne domin mika masa bindigogin tun da yanzu zai bar gidan gwamnati kuma abokin hamayyarsa ne zai gaje sa.

Wanda gwamna Amosun yaso yaci zabe, Adekunle Akinlade, na jam'iyyar APM ya sha kayi a hannun gwamna na yanzu, Dapo Abiodun, na APC wanda ya laburta cewa magabacinsa bai bar ko sisi a asusun gwamnatin jihar ba.

Bayan ganawar Amosun da kwamishanan yan sanda, Makama tare da wasu jami'an yan sanda suka kwashe dubunnan makamai da harsasan da gwamnan ya boye.

KU KARANTA: Kawai ka mika kanka ga hukumar yaki da rashawa - Kungiyar yan fafutuka sun shawarci sarkin Kano

Daga cikin abubuwan da aka tarar sune bindigogi kirar AK47 guda 1000, carbin harsasai milyan hudu, rigar kare harshashi 1000, da motar mara jin harsasai.

A lokacin mika makaman, Amosun ya ce an siya wadannan makamai ne domin kare al'ummar jihar kuma ya yanke shawarar ajiyesu a gidan gwamnati saboda yana tsoron abinda jami'an tsaro za suyi da shi idan aka basu

Daga baya aka kai makaman hedkwatan hukumar yan sanda dake Elewe-Eran, Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Makonni hudu bayan haka, manyan jami'an tsaron Najeriya sun mamakin ta yaya gwamnan farin hula zai ajiye dubunnan makamai a gidan gwamnati. Suna mamakin shin me yasa har yanzu ba'a damke gwamna Amosun ba saboda abinda yayi ya sabawa dokar kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel