An damke masu leken asiri da kaiwa yan bindiga kayayyaki a Sokoto

An damke masu leken asiri da kaiwa yan bindiga kayayyaki a Sokoto

Hukumar sojin Najeriya ta yi arangama da wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri da masu kai musu kayayyaki a kasuwan Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birnin jihar Sokoto.

Game da cewar kakakin hukumar, Kanal Sagir Musa, ya ce dakarun sojin atisayen Operation HARBIN KUNAMA III sun yi wannan kamu ne a harin bazatan da jami'an soji suka kai wa yan bindigan cikin jihar Sokoto da kewaye ranar 23 ga Yuni, 2019.

Sun kai harin ne bisa ga rahoton leken asirin da suka samu cewa yan leken asirin masu garkuwa da mutanen sun shigo kasuwa siyayya.

KU KARANTA: Kawai ka mika kanka ga hukumar yaki da rashawa - Kungiyar yan fafutuka sun shawarci sarkin Kano

Daga cikin wadanda saka kama sune:

(1) Malam Ibrahim - Shahrarren mai kaiwa yan bindiga labari da kuma amsan kudin fansa

(ii) Mallam Ashiru Goni — Shahrarren mai kaiwa yan bindiga kayayyaki ciki da wajen jihar Sokoto

(iii) Mamman Taratse — Shahrarren mai sayar da shanun sata a ciki da wajen jihar Sokoto

An damke masu leken asiri da kaiwa yan bindiga kayayyaki a Sokoto
Sokoto
Asali: Facebook

Hakazalika, jami'an sojin sun yi batakashi da da yan bindiga a kauyan Magira bayan samun labari. An hallaka yan bindiga da dama kuma an yi rashin soja daya.

Ya ce kwamandan 8 Division, Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki, a madadin babban hafsan soji Laftanan Janar Tukur Buratai, ya yabawa sojin kan jajircewan da sukayi wajen samun wannan nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel