Dankwambo ya siyarwa da kanshi motocin miliyan 300 akan miliyan 12

Dankwambo ya siyarwa da kanshi motocin miliyan 300 akan miliyan 12

-Gwamnan jihar Gombe ya ce babu wanda ke yima tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo bita da kulli

-Babban mai ba gwamnan shawara akan harkokin watsa labarai Isma'il Misilli ya ce tsohon gwamnan ya saida ma kanshi motoci wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 300 akan kudi Naira miliyan 12

-Misilli Ismail ya ce sun rasa gane dalilin da yasa za ayi tunanin ana yima gwamnana bita da kulli bayan da binciken yan kwamitin kwato kadarorin jihar ya tabbatar da hakan

Babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara kan harkokin watsa labarai, Ismail Misilli ya musanta zargin da ake yi na cewa suna bin tsohon gwamnan jihar da bita da kulli akan sayar da kayan gwamnati na miliyoyin Nairori.

Jawabin da Isma’il ya sanyawa hannu ya turoma Legit.ng, ya bayyana cewa ya zama dole a fadi wa duniya cewa gwamnan Inuwa Yahaya dunbin mutane ne suka zabe shi a fadin kananan hukumomi 11 na jihar.

KARANTA WANNAN: Kudin kasar wajen Najeriya ya haura Dala Biliyan 45 – Inji CBN

Ya kuma kara da cewa gwamnana na samun so da kauna daga mutanenshi.

Isma’il ya ce gwamnatin jihar ta rasa gane dalilin da yasa ake tunanin ana ma tsohon gwamnan bita da kulli duk da cewa binciken yan kwamitin kwato kadarorin jihar ya tabbatar da cewa akwai hannun tsohon gwamnan a cikin sayar da kadarorin jihar

Isma’il ya ce "Abun shine, idan aka dora maka alhakin rikon jama’a a matsayin shugaban karamar hukuma, gwamna ko shugaban kasa, ya zama dole kayi bincike don gano inda matsaloli suke."

Isma’il ya kara da cewa kwamitin kwato kadarorin jihar wanda Peter Bilal ke jagoranta, an dora masu alhakin gano yadda akayi gwanjon kadarorin jihar a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo, wanda hakan yasa dole akwai muhimman tambayoyi da za ayi.

“A duniya ina ne za a ce ka siyar da motoci biyar da kudinsu ya haura Naira miliyan 300 ga mutum guda (kai kanka) akan kudi Naira miliyan 12, ta yadda zaka bar saban gwamna da tsofaffin motoci? Duk masu korafi to wadanda suka amafana da wannan rashin gaskiyar ne.”

“Daya daga cikin masu haushin karnukan, a boye ya maido nashi saboda baya so a kunyata shi, amma yana zuga wasu kada su maido.”

Ya kara da cewa wasu daga cikin masu korafin na cewa ba zasu maido motocin ba har sai an biyasu kudin su na sallama daga aiki. Ya ce “Muna maganar sababbin motoci ne dal.”

“Kaje ka binciki kudaden motocin a kasuwa kuma ka binciki nawa aka saida su ga mutanen tsohuwar gwamnati.”

“Ina so in fahimtar da mutane cewa mu fa kwamiti kawai muka nada bamu kai kotu ba, saboda haka duk masu cewa muna yima tsohuwar gwamnati bakin fenti cewa ta aikata rashawa to ba gaskiya bane, saboda wannan aikin kotu ne da sauran hukumomin da ke da alhakin su bayyana hakan.”

Isma’il ya kara da cewa afadin duniya ana gwanjon kaya ne idan da dalili na gaskiya. Ya ce “Mafi yawan motocin da akayi gwanjonsu sababbi ne dal. Ban san wani bangare na duniya ba da ake yin gwanjon sababbin kayayyaki a wulakance.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel