Rikicin Amurka da Iran: Yayinda da kasar Rasha ta alanta niyyar taimakawa Iran, Sakataren Amurka ya tafi Saudiyya tattaunawa
Yaki gadan-gadan na cigaba da kunno kai tsakanin Amurka da Iran yayinda wasu kasashe masu karfin mulkin soja suka fara nuna wadanda zasu taimakawa.
Rahotanni sun nuna cewa kasar Rasha ta bayyana niyyar taimakawa Iran wajen saukake takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran.
Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov, ya bayyana ranar Litinin cewa Rasha za ta dauki mataki wajen dakile sabbin takunkumin da Amurka ke kokarin kakabawa Iran.
A jawabin nasa da TASS da RIA suka ruwaito, Ryabkov bai bayyana irin matakin da Rasha za ta dauka ba. Ya ce a maimakon kokarin makawa Iran takunkumi, kamata yayi Amurka ta fara neman yadda za'a yi sulhu.
KU KARANTA: Yan Najeriya 42 suka kashe kansu cikin shekarar nan - Rahoton Lissafi
A bangare guda kuma, sakataren wajen Amurka, Mike Pompeo, ya dira kasar Saudiyya, babbar abokiyar Amurka domin tattaunawa kan rikicin Iran.
Ana sa ran Pompeo zai gana da Sarki Salman da yarima, Mohammed bin Salman a birnin Jiddah, kafi tafiya kasar UAE, jami'an Amurka sun tabbatar da haka.
Kafin tafiyarsa Saudiyya, sakataren Amurka Pompeo ya fara shirin hada kan wasu kasashe domin su yiwa Iran taron dangi
Pompeo yace: "Za mu tattauna dasu (Saudiyya da UAE) kan yadda zamu hada kai da kasashen nahiyar Asiya da Turai domin take kasar da ta fi kowa daukar nauyin yan ta'adda."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng