Dankari: 'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya na barazanar shiga yajin aiki kan albashi
- 'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda albashi
- Da fari dai ya kwallom sun sha alwashin nade kafa a otel dinsu domin tilastawa jami'an kasar biyan su ladan wasannin da suka yi a gasar cin kofin duniya ta mata
- Sai dai bayan tattaunawa da suka yi, hukumar NFF ta yi alkawarin biyansu kudadensu tun daga 2016
'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya sun yi barazanar nade kafa a otel dinsu domin tilastawa jami'an kasar biyan su ladan wasannin da suka yi a gasar cin kofin duniya ta mata.
A hira da BBC tayi da daya daga cikin 'yan wasan ta shaida wa bayyana cewa sun yi wani zama na musamman da daddare a otel din Grenoble tare da shugabar Hukumar Kwallon Lig ta mata, Aisha Falode.
Bayan shafe awowai ana tattaunawa, Hukumar Kwallon Kafa ta NFF ta yi alkawarin biyansu dukkan basussukan da suke bi tun daga shekarar 2016.
Daga bisani 'yan wasan suka amince su bar otel din.
Wata 'yar wasan ta daban ta sake bayyana cewa sun sake yin wani taron da shugabannin hukumar ta NFF.
KU KARATA KUMA: Za mu tsamo sojojin da basu shirya yaki da Boko Haram ba sannan mu fatattake su - Buratai
A sakamakon haka, uku daga cikin 'yan wasan ba su samu damar komawa kulob dinsu ba kamar yadda aka tsara saboda sun makara har jirgi ya tashi ya bar su.
Rahotanni sun ce kudaden da suke bi har da na shiga gasar wadanda Hukumar FIFA ke bayarwa, sai dai NFF ta ce kudin ba su zo hannunta ba tukunna domin sai an kammala gasar FIFA ke bayarwa.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng