Wani bam ya tashi a masallacin 'yan Shi'a ya kashe mutane 7 ya jikkata sama da 20
- Bam ya tashi a masallacin yan uwan Musulmai na Shi’a da ke yankin gabashin Baghdad a ranar Juma’a
- Lamarin yayi sanadiyar mutuwar mutum bakwai sannan ya jikkata sama da mutane 20
- Zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin
Wani bam da ya tashi a masallacin yan uwan Musulmai na Shi’a da ke yankin gabashin Baghdad a ranar Juma’a, 21 ga watan Yuni yayi sanadiyar mutuwar mutum bakwai sannan ya jikkata sama da mutane 20.
Wata babbar majiya na yan sanda ta bayyana cewa tashin bam din ya afku ne a makota da Baladiyat, sannan cewa anyi amfani da abun dana bam ne wajen kaddamar da harin, wanda zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Majiyar ta bayyana cewa ana sanya ran za a samu karin adadin wadanda suka mutu domin wadanda suka jikkata na a cikin wani mawuyacin hali a yanzu haka.
An tattaro cewa ba kasafai ake samun irin wannan harin ba a wajen bautar yan Shi’a ba a babbar birnin kasar Iraqi.
KU KARANTA KUMA: Hankula sun tashi yayinda yan bindiga suka sake kai hari jihar Taraba
A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa shi ko kadan baya fatan Allah ya hada su yaki da kasar Iran, amma kuma ya yiwa kasar ta Iran gargadi, inda ya bayyana mata cewa idan har yaki ya hado su to babu makawa za ta shafe ta daga doron kasa.
A lokacin da yake hira da gidan talabijin na NBC a jiya Juma'a, shugaban kasar ya kara yiwa kasar ta Iran maganar cewa kasar Amurka a shirye take domin ta tattauna da ita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng