Amurka ta sanya dokar dandake masu lalata da kananan yara

Amurka ta sanya dokar dandake masu lalata da kananan yara

- Jihar Alabama da ke kasar Amurka ta kafa doka akan duk mutumin da aka kama da laifin lalata da kananan yara

- Hukuncin shine za a yi wa wanda aka kama da laifi dandaka, ta hanyar bashi magani ko allurar rage sha’awar jima’i

- Za a dauki tsawon wasu watanni ana ba mai shi maganin bayan an tsare shi, sannan daga karshe zai biya kudin maganin da aka yi masa

Rahotanni sun kawo cewa an kafa sabuwar doka a jihar Alabama da ke kasar Amurka akan duk mutumin da aka kama da laifin lalata da kananan yara. Hukuncin shine za a yi wa wanda aka kama da laifi dandaka, ta hanyar bashi magani ko allurar rage sha’awar jima’i.

A bisa dokar, duk mutumin da aka kama da lalata yarinya karama yar kasa da shekara 13 za a fara bashi magngunan rage sha’awar har tsawon wasu watanni kafin a sako shi daga wajen da aka tsare shi.

A halin da ake ciki, kotu ce za ta tabbatar ko akwai bukatar wannan dokar nan gaba ko babu.

Akwai jihohi bakwai wadanda suka hada da: Louisiana da Florida a Amurka wadanda duk suke da irin wannan dokar ga duk wanda aka samu da laifin yin lalata da karamar yarinya sai an basu magungunan rage saha’awar yin jima’i.

A ranar Litinin da ta wuce ne Gwamnan Alabama Kay Ibey, ta rattabawa kudirin dokar hannu.

“Wannan wani mataki ne kare rayuwar yara mata a jihar Alabama,” in ji Gwamnar.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Iran da Amurka: Trump ya tattauna da Yariman Saudiyya

Duk mai laifin da aka kama sai ya biya kudin maganin da aka yi masa. Dan majalisar wakilai na Jam’iyyar Republican Stebe Hurst, ne ya gabatar da kudirin dokar.

Stebe ya ce ya dade yana jin korafin kungiyar kare hakkin yara ta yadda ake cin zarafin ’yan mata kanana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel