Yadda wani boka da abokinsa suka kashe matar aure mai neman asirin kudi

Yadda wani boka da abokinsa suka kashe matar aure mai neman asirin kudi

Bosede Oguntade, matar aure mai shekaru 25 a duniya ta hadu da ajalinta a hannun wani malamin tsibu, Dotun Ogunlade da akafi sani da Arole Jesu da abokinsa Mutiu a garin Ibarapa da ke jihar Oyo.

Oguntade ta tafi wurin Ogunlade ne domin neman maganin yadda za ta warware matsalolin aure da kuma neman arziki.

Ta tuntubi shi ne ta shafin sada zumunta na Facebook inda ya yi alkawarin zai taimaka mata warware matsalolin ta kuma suka shirya haduwa a ranar 31 ga watan Mayun 2019.

DUBA WANNAN: Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Bosede ta bar gidanta da ke jihar Kwara domin zuwa wurinsa amma bata san cewa ya hada baki da abokinsa Mutiu domin su kashe ta ba. Sun datse kan ta da hannayen ta su kayi amfani da su wurin tsafi na kudi sannan suka kone sauran gangan jikinta.

A yayin da ya ke magana da manema labarai, Oguntade ya ce: "Ni da matar (Bosede mun dade muna tattauna ta Facebook tun Janairun wannan shekarar. Daga baya na gayyace ta zuwa Igboora. Abokina, Mutiu ya dade yana min korafin halin da ya shiga na kuncin rayuwa. Ya ce min a shirye ya ke ayi masa asirin kudi. Saboda haka zai nayi amfani da matar domin in masa asirin.

"Bayan matar da taho daga Ilorin, na kawo ta gida na a ranar 31 ga watan Mayun wannan shekarar. Na bata maganin barci a lokacin da ta ce min jikin da na ciwo. Bayan tayi barci na datse kanta da hannayen ta. Daga baya na kone kanta domin yin asirin kudi."

Rundunar 'Yan sanda ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel