'Yan fashi da makami sun yi wa farfesa kisar gilla a gidansa

'Yan fashi da makami sun yi wa farfesa kisar gilla a gidansa

Wasu 'yan fashi da makami da ba a gano ko su wanene ba sun kashe wani malami da ke koyarwa a Jami'ar Jihar Rivers, Farfesa Emmanuel Amadi.

Kafin rasuwarsa, marigayi Farfesa Amadi malami na a tsangayar nazarin kananan hallitu a jami'ar ta jihar Rivers.

Mai magana da yawun Rundunar 'Yan sandan jihar, DSP Nnamdi Omoni ya tabbatar da afkuwar lamarin a birnin Fatakwal a ranar Alhamis, ya ce marigayin ya rasu ne sakamakon raunin da 'yan fashin suka yi masa.

DUBA WANNAN: Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Omoni ya ce 'yan fashin sun kashe malamin ne bayan ya gane daya daga cikinsu da suka zo masa fashin.

"Cikin bakin ciki, mun tabbatar da rasuwar Farfesa E.N. Amadi na Jami'ar Jihar Rivers. An kashe Farfesa Amadi ne a ranar Laraba, 19 ga watan Yuni misalin karfe 04 na yamma yayin da 'yan fashi da makami suka kai hari gidansa."

"Ya gane fuskan daya daga cikin 'yan fashin hakan ya sa suka dawo suka buga masa wani karfe a kansa hakan yasa ya fadi sumame."

Ya ce an tabbatar da rasuwar marigayin ne bayan an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami'ar Fatakwal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164