Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da Talon kan rikicin siyasa a kasar Benin

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da Talon kan rikicin siyasa a kasar Benin

- Shugaban kasa Buhari na cikin ganawa da shugaban kasar Benin, Patrice Talon

- Buhari ya tarbi Talon a fadar Shugaban kasar da ke Abuja da misalin karfe 11:30 na safe

- An tattaro cewa ganawar nasu baya rasa nasaba da rikicin da ke kewaye da gyara dokar kundin tsarin zaben kasar da kuma zaben majalisar na watan Afrilu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa da takwaransa na kasar Benin, Patrice Talon a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaba Buhari ya tarbi Talon a fadar Shugaban kasar da misalin karfe 11:30 na safe.

Tuni dai Shugabannin biyu suka shiga ofishin Shugaban kasar domin ganawar.

An tattaro cewa ganawar nasu baya rasa nasaba da rikicin da ke kewaye da gyara dokar kundin tsarin zaben kasar da kuma zaben majalisar na watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Takaitaccen tarihin sabon shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta sirri da gwamnan jihar Kano, Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje a fadar Aso Villa.

Kamar yadda Bashir Ahmaad, wanda ya yi aiki a matsayin Hadimin shugaban kasar tsakanin 2015 zuwa 2019 ya sanar, Buhari ya zauna da Abdullahi Ganduje ne a Ranar 19 ga Watan Yuni.

Malam Ahmaad da ya bada wannan sanarwa a jiya Laraba, bai yi wani karin bayani game da abin da a ka tattauna ba. Kafin nan dama duk gwamnonin kasar sun gana da shugaban kasa Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel