"Ba Za Mu Yarda ba"; 'Yan Bindiga Sun Ga Bala'in da Ya Fi Karfinsu a Zamfara

"Ba Za Mu Yarda ba"; 'Yan Bindiga Sun Ga Bala'in da Ya Fi Karfinsu a Zamfara

  • Mazauna Birnin Tudu a Ƙaramar Hukumar Gummi ta Zamfara sun ce sun kashe ’yan bindiga sama da 30 a fafatawar da ta ɗauki kwanaki uku
  • An ruwaito cewa mutane uku sun mutu a cikin garin, wasu kuma suka samu raunuka, yayin da aka kashe wasu mutane a wajen ƙauyen
  • Rundunar ’yan sandan Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro ga mazauna yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Mazauna garin Birnin Tudu da ke Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara sun ce sun kashe ’yan bindiga sama da 30 bayan kwashe kwanaki uku suna fafatawa da su.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun zo da ɗaruruwan babura, suka kewaye ƙauyen sannan suka fara harbe-harbe.

'Yan bindiga sun fafata da mutanen gari a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin garin da ya zanta da jaridar Daily Trust bisa sharaɗin ɓoye sunansa, ya ce maharan sun yi wa al’ummar kwanton bauna ne a lokacin da suka rage sa ido kan tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki ayarin motoci a Sokoto, an kashe malami da wasu mutane

Ya ce al’ummar sun saba kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin kare kansu, amma a wannan karon sun yi tunanin komai yana tafiya daidai.

’Yan bindiga sun kewaye ƙauyen

Mazaunin ya ce maharan sun isa garin da misalin ƙarfe 10:00 na safe ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2026 a lokacin da wasu mazauna yankin suka tafi gonakinsu domin girbe amfanin gona.

Ya bayyana cewa kafin su fahimci abin da ke faruwa, ’yan bindigar sun riga sun kewaye ƙauyen ta kowane ɓangare.

A cewarsa, mutane uku ne ke hawa kowane babur, kuma sun yi amfani da babura sama da 100 wajen kai harin. Ya ce ya iya ƙirga babura 71 da kansa daga inda ya ɓuya.

Bayan shigarsu garin, maharan sun riƙa harbe-harbe, tare da fasa shaguna da kwashe kayayyaki.

Mutumin ya ce al’ummar sun yanke shawarar tunkarar maharan maimakon guduwa daga gidajensu.

Ya bayyana cewa sun gode wa Allah saboda wasu daga cikinsu sun shirya kare al’ummar, domin ba sa son barin gidajensu su zama ’yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Houthi ta zafafa hare hare kan Saudiyya, ta yi gagarumar barna

An kashe mazauna garin

Mutumin ya ce fafatawar ta yi sanadin mutuwar mutane uku a cikin garin, yayin da wasu mutum uku suka samu karaya a ƙasusuwansu, wani kuma ya samu raunin harbin bindiga.

Ya ƙara da cewa maharan sun sake dawowa domin wata fafatawa ta biyu a lokacin da mazauna garin ke raba batir ɗin fitilun tocila.

A cewarsa, al’ummar sun sake tunkarar su, daga bisani suka fatattake su zuwa gabashin ƙauyen. Ya ce maharan suna da yawa kuma dukansu suna ɗauke da makamai.

Sai dai maharan sun yi nasarar kwashe shanun da suka sace daga wasu al’ummomin da ke maƙwabtaka, amma ba su sace dabbobin Birnin Tudu ba.

An ce maharan sun yi amfani da ƙungiyoyi uku

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun rarrabu zuwa ƙungiyoyi uku a lokacin harin.

A cewarsa, ƙungiya ta farko ta ƙunshi babura sama da 71, inda mutane uku ke hawa kowane babur. Ƙungiya ta biyu kuma tana tafiya da shanun da aka sace, yayin da ta uku ke biye da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin da ya ritsa da jariri da wasu mutane a Kaduna

Ya ce maharan sun yi amfani da na’urorin sadarwa wajen tuntuɓar abokansu da ke cikin dazukan da ke kewaye da yankin, suna umartar su da su sake haɗuwa.

Mazaunin ya ce da farko sun ƙirga gawar ’yan bindiga 11 da suka kashe, amma yayin da suke ƙoƙarin kwace bindigoginsu, wasu mahara suka sake kai musu hari.

Ya bayyana cewa sabon harin ya hana su kwato ƙarin makamai da za su yi amfani da su wajen kare kansu.

’Yan banga sun shirya dakile sabon hari

Mazaunin ya bayyana cewa a safiyar Alhamis, 22 ga watan Oktoban 2026 al’ummar sun samu bayanan sirri cewa ’yan bindigar na tunkaro su daga yammacin yankin.

Wannan bayanin ya sa mazauna garin da ’yan banga suka fara shirin fuskantar wani hari.

Ya ce sun kuma samu rahotannin cewa maharan sun sace shanu daga ƙauyen Sabon Garin Kaddagi, kuma suna kan hanyar zuwa wani daji mai suna Kwartaga.

A cewarsa, ’yan banga sun tabbatar da ganin maharan a yankin, sannan suka yi kwanton bauna domin hana su shiga garin.

Daga bisani, bayanan da al’ummar suka samu sun nuna cewa adadin ’yan bindigar da aka kashe a fafatawar ya haura 30.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro tare da sace hamshakin attajiri a Plateau

Mazaunin ya ƙara da cewa baya ga mutane uku da aka kashe a cikin Birnin Tudu, an kuma kashe wani mutum a wajen garin, yayin da aka samu rahoton mutuwar wani mutum a Dantsullutu.

Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

’Yan sanda sun tabbatar da harin

Da Legit Hausa ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Yazid Abubakar ya ce rundunar ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da kuma samar da isasshen taimakon ’yan sanda ga mazauna garin.

“Eh ya lamarin ya faru, kuma mun ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa sun samu isasshen taimako ’yan sanda.” In ji shi.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani sabon malamin makaranta a Jihar Sokoto, Maniru Sa’adu Imam.

'Yan bindigan sun kashe shi ne sa’o’i kaɗan bayan ya halarci aikin tantance bayanan ma’aikata domin fara karɓar albashi a cikin birnin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng