Rikici gadan-gadan: Iran ta baro jirgin leken asirin Amurka
- Tun hawan Donald Trump mulki, Iran da Amurka suka shiga takun saka
- A kwanakin baya, Amurka ta kakabawa Iran takunkumi da kan shafi tattalin arzikinta
- Da alamun yaki zai iya faruwa tsakanin wadannan kasashe masu karfin nukiliyan biyu
Da safiyar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2019 Kasar Iran ta baro jirgin leken asirin kasar Amurka yayinda rikici ke cigaba da kunno kai tsakanin manyan kasashen guda biyu.
Yayinda jami'an tsaron kasar Iran na ikirarin cewa jirgin Amurkan ta shiga huruminta shi yasa suka barota, amma jami'an Amurka sun ce ba haka bane, jirgi bata shiga hurumin Iran ba a lokacin.
Har yanzu ba'a menene gaskiya lamarin ba.
KU KARANTA: Hukumar yaki da rashawa ta sammaci uwargidar Sarki Sanusi, matan Ado Bayero, da wasu masu saurauta
Shafin labaran jihar Hormozgan tace: "Mun baro jirgin leken asirin kasar Amurka. Mun barota ne lokacin da ta shigo hurumin kasar Iran kusa da Koumobarak."
Wannan abu da ya faru shine fito-na-fito na farko tsakanin Iran da Amurka yayinda aka fara cacan baki tsakanin kasashen guda biyu tun hawan mulki shugaba Donald Trump da sanyawa Iran takunkumi.
Amma kasar Amurka ta karyata rahoton Iran cewa an shiga huruminta.
Kakakin hukumar sojin Amurka, Bill Urban, yace: "Babu wani jirgin leken asirin da ya shiga hurumin Iran."
Kwamandan hukumar tsaron Iran ya ce wannan abu da kasar tayi sako ne ga kasar Amurka.
Janar Hossein Salami yace Iran ba tasa wani niyyar yaki da wani kasa amma fa shirye take da gwabzawa da kowa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng