An tashi: Dambazzau ya lallasa Kawu Sumaila a kotu
- Kotun daukaka kara ta raba gaddama tsakanin Kawu Sumaila da Dambazzau
- Shamsudden Dambazzau ya samu nasara
A ranar Laraba, Kotun daukaka kara dake zaune a Kaduna ta yi watsi da karar tsohon hadimin shugaba Buhari, AbdulRahman Kawu Sumaila, inda yake kalubalantar shari'ar babbar kotun tarayya ta jihar Kano.
Shamsudden Dambazzau, wanda 'da ne ga ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazzau ya samu nasara kan Kawu Sumaila a kotun daukaka kara kuma shine zababben mai wakiltar mazabar Takai/Sumaila a majalisar wakilan tarayya.
Alkalan kotun sun yi ittifakin cewa karar da Kawu Sumaila ya shigar ba tada gaskiya kuma an yi watsi da ita.
KU KARANTA: Dangote ya bada tallafin N60m ga mata yan kasuwa da marasa galihu a jihar Katsina
A ranar 23 ga watan Oktoban 2018, Shamsuddeen Dambazau ya shigar da kara babban kotun tarayya dake jihar Kano inda yake kalubalantar zaben Kawu Sumaila.
Ya bayyana cewa shine wanda ya cancanci takara kujerar majalisan karkashin jam'iyyar APC saboda Kawu Sumaila bai yi musharaka a zaben fidda gwani ba.
Bayan zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ta kujerar Sanata mai wakiltan Kano ta kudu tsakanin Sanata Kabiru Gaya da Kawu Sumaila, inda Sumaila ya sha kayi, manyan APC a jihar sun yi sulhun cewa a baiwa Kawu Sumaila damar takara kujerar majalisar wakilai.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng