Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta rasa saurayinta bayan ta saka shi a caca

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta rasa saurayinta bayan ta saka shi a caca

- Tsautsayi ya sanya wata budurwa ta rasa saurayinta bayan ta sanya shi a caca, a ganinta cewar ta gama siye zuciyarsa

- Sai dai kuma ashe abun ba haka yake ba, domin kuwa cikin kankakin lokaci budurwarda ta kalubalanceta ta kwace saurayin nata

- Inda daga baya ta zo tana bata hakurin cewa tayi hakuri ta kwace mata saurayi domin kuwa yanzu ko ganeta ba zai yi ba idan tayi masa magana

Wani saurayi mai suna Akin yayi suna sosai a shafukan sada zumunta, musamman Twitter, hakan ya biyo bayan yadda wata budurwa wacce ta sanya sunanta kamar haka @DidenIye, ta shiga shafinta na Twitter ta wallafa cewa za ta iya jawo hankalin saurayin kowacce budurwa.

Tsautsayi sai yasa wata budurwa mai suna @AnayoAnn ta mai da mata da martani akan rubutun da ta wallafa, inda ta amince da sharadinta kuma ta kalubalance ta, saboda ganin cewa ta yadda da saurayinta.

KU KARANTA: Ajali in yayi kira: Wani birkila ya yiwa karuwarshi mari daya tal, ta sheka lahira

Budurwar wacce ta fara rubutun a shafin Twitter sai ta nemi dayar budurwar da ta kalubalance ta akan ta ba ta lambar saurayinta, tsautsayi ya kara sawa ta bayar da lambar.

Ba jimawa ta fara hira da saurayin, ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai gashi ta aika mata da sako cewa, "Kiyi hakuri na kwace miki saurayi, domin yanzu ko gane ki ba zai yi ba."

Ga hotunan yadda hirar tasu ta kaya da saurayin nata a cikin manhajar WhatsApp wanda suka yi da turanci:

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta rasa saurayinta bayan ta saka shi a caca
Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta rasa saurayinta bayan ta saka shi a caca
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel