Yanzu-yanzu: Dakin kwanan dalibai mata daya tilo da ya rage ya kama Gobara a Adamawa

Yanzu-yanzu: Dakin kwanan dalibai mata daya tilo da ya rage ya kama Gobara a Adamawa

- Dalibai za su koma gida yayinda dakin kwanansu da ya rage ya ci bal-bal

- Irin wannan abu ya faru a makarantar a shekarar 2018 inda dakin kwana ya kone

- Babu dalibar da ta jikkata a gobarar

Dakin kwanan dalibai mata daya tilo da ya rage a makarantar sakandaren mata GGC Mayo Belwa, jihar Adamawa ya kama da wuta.

Makarantar ta kasance tana da dakunan kwanan dalibai biyu amma gobara ta cinye daya a shekarar 2018.

Yayinda ake shirye-shirye gyara wanda ya kone, dayan ya kama da gobara da safiyar yau Talata, 18 ga watab Yuni, 2019.

Wani ma'aikacin karamar hukumar Mayo Belwa, Aliyu Isah, wanda yayi magana da manema labarai a wayan tarho ya bayyana cewa: "Dakin kwanan dalibai daya tilo da ya rage ya kama da wta. Wuta ya cinyeshi ga baki daya."

Aliyi Isah, wanda magatakarda ne a majalisar dokokin Mayo Belwa yace har yanzu ba'a san abinda ya sabbaba gobarar ba amma ana kyautata zaton matsalar wutan lantarki ne.

Yace: "Abin takaicin ne saboda yanzu dole ne daliban su koma gida. Wannan shine dakin kwana daya da ya rage tun lokacin da na biyun yayi gobara a bara."

Ya kara da cewa babu dalibar da ta gobarar ya shafa ta konewa ko samu rauni.

Makarantar matan tana karamar hukumar Mayo Belwa, kudancin jihar Adamawa, da nisan kimanin kilomita 70 da birnin jihar, Yola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel