Allahu Akbar: Yau Dr. Mamman Shata yake cika shekaru 20 da rasuwa, ga takaitaccen tarihinsa
A yau Talata, 18 ga watan Yuni yayi daidai da ranar Dr. Mamman Shata ke cika shekaru 20 da rasuwa. Hakan ya sa muka yi amfani da wannan dama wajen kawo maku dan takaitaccen tarihin rayuwarsa.
An haife Mamman Shata a garin Musawa da ke jihar Katsina, a cikin shekarar 1922. A shekarar ne kuma Turawan Birtaniya suka shimfida hanyar jirgin kasa a yankin rewacin Najeriya.
Sunan kakanninsa na wajen mahaifinsa Bako da Hadiza (Dije), amma ita an fi kiranta da sunan ‘Maikitso’. Su, Fulani ne na ruga kuma mahalba.
Bako na daga cikin zuriyar su Musa da su ka taso daga Sanyinna ta kasar Sakkwato a yau, cikin shekarar 1810.
Sunan mahaifiyarsa Binta, sabanin sunan Lariya da wasu littattafan da aka wallafa akan mawakin a baya da su ka bayyana. Sai dai kumaa Lariya ta kasance kanwar mahaifiyarsa, kuma ita ta rene shi, ta goya shi har ya isa yaye.
Fulanin daji irin na da su na yawan boye sunan mahaifiya saboda kawaici ko gudun asiri, sammu ko dai wani abu makamancin wannan, don da sunan uwa ake yi wa mutum sammu ko mugun abu har a samu galabarsa.
Tun yana dan yaro yake nuna wasu abubuwa na al’ajabi da su ke nuna alamun a gaba za a yi mutum muhimmi a Duniyakuma gagararre.
Ya yi kiwon dabbobin gida tunda ya tashi ya ga mahaifinsa na kiwo, kafin ya shiga makarantar boko a Musawa cikin 1932. Sai kakarsa Dije ta cire shi. Daganan sai ya fara tallar goro, har ta kai yana bin kasuwannin kudancin lardin Katsina, kamar yadda kuma ya dan taba tallar alewa, amma tallar alewar ba ta yi karfi kamar tallar goron ba. Da tallar goro aka fi saninsa sosai.
A kasuwar Sukuntuni (kasar Rimaye ce ta jihar Katsina) wasu Fulani su ka ce masa ‘kai mai-sha-ta alewa, kawo alewar nan’ saboda duk inda ya je yana tallabe da farantin alewar sai ya ce ‘sha-ta alewa’ (watau ‘ku sha alewa’), Daga nan sunan Shata ya bi shi har inda yau ta ke.
Shata ya soma waka daga wani yayi da ya taso a Arewacin Najeriya ta yi wa wata yunwa da aka yi a lokacin waka, mai suna Takojilo, cikin 1935. Wasu shekaru 5 masu zuwa, wakar sa ta habaka ainun, har Magajiyar Musawa, wata da ta yi hidima a gidan Sarkin Musawa Usman Liman ta yi sanadiyyar zuwan sa Ketare cikin 1940 a dalilin auren Bayi,wata mata da aka rika a gidan Sarkin Musawa din da kuma Balan Magaji, wani yaron maigarin Ketare kuma dillalin zannuwan mata, inda a Ketare Shata ya hadu da Danmaihura, wani maroki kuma mawakin Asawwara, har ya zama ubangidansa.
Daga bisani kuma ya koma hannun Isan Torobi, wani fitacce, mai cinikin gyada da auduga kuma yaron wani kwara ana kiransa Kwastan mutumin Lebanon da ya yi sansani a Malumfashi. Inuwa ko Mammada daya daga cikin ‘ya’yan Isan Torobi ya yi ubangida da Shata daga baya, har su ka dade tare.
KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban INEC, Jega yayi magana akan rigimar na’urar INEC
An tattaro cewa wakokin Mammada da ya fara yi masa cikin 1940, su suka fara fiddo Shatan a idon Duniya,ko da yake ba a kan sa ya fara yin irin samfurin wakokin ba, amma a kan sa wakokin suka shahara.
Cikin watan Yunin 1943 kuma sai Abdullahi Inde wanda ya zama Magajin Musawa kuma babban dan Sarki Musawa Usman Liman ya dauke shi ya maishe shi Bakori da zama, inda ya sada shi da ‘ya’yan sarakuna na wancan zamanin. Nan kuma shekararsa 11.
Daga Bakori Shata ya ida zama gagararre, wanda sunansa ya bazu ko’ina ciki da wajen Kasar nan kamar ‘wutar-bazara’, kuma ya buwaya. Tun cikin 1948 mutanen Kontagora su ke ganin mawakin na rabawa ta can ya na tafiya kurmi da wasu sassan Gwalkwas.
Sannan daga Bakori ya tafi Legas cikin 1951 inda ya amsa gayyatar Badejo Gramaphones, masu daukar faya-fayi suna kaiwa Gwalkwas su na wankewa. Daga Bakori kuma ya ragade kusan kasar Katsina da wasu sassan Kano da Sakkwato da kewaye har da su Abidjan da Dahome da Ghana da Nijar da aikin waka.
A cikin 1952 Shata ya kara samun ci-gaba a hidimar waka, don lokacin ne ya tafi bukin ‘yan Sarki na Kano, amma kuma bukin ‘yan Sarki da ya yi bayan shekara 2 watau 1954 shi ne dalilin zaman sa Kano, daga 1954 zuwa 1959, inda ya yi zaman shekara biyar da wata shida.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng