Allah ya haskaka makwanci: An yi jana'izar Muhammad Mursi da safen nan

Allah ya haskaka makwanci: An yi jana'izar Muhammad Mursi da safen nan

An gudanar da jana'izar zababben shugaban kasar Misra na farko, Mohammad Mursi, da safiyar Talata, 18 ga watan Yuni a Kahira, babbar birnin kasar bayan rasuwarsa yayinda yake gurfana a kotu ranar Litinin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi kira ga bincike mai zaman kanta kan abinda ya kai ga rasuwar tsohon shugaban kasan da akayiwa juyin mulki a shekarar 2013.

Daya daga cikin lauyoyinsa, Abdel Moneim Abdel Maksoud yace: "an birneshi a Medinat Nasr, kudancin Kahira, kuma iyalansa sun hallarar."

An gurfanar da shi a kotu ne bisa ga zargin hada baki da wasu kasashen waje da yan bindiga.

KU KARANTA: Yanayin kasa: Ka saurari shawarar Obasanjo, kungiyar Fulani ta fada wa Buhari

Majiya tyace: "Kotu ta bashi daman yin magana na tsawon mintuna biyar... sai ya fadi kasa cikin keji kuma aka kaishi asibiti a lokacin."

"Ya isa asibiti misalin karfe 4:50 na yamma kuma babu wani alamun rauni a jikinsa."

Daya daga cikin lauyoyin Mursi, Osama El Helw, ya bayyana abinda ya faru a lokacin da ya samu labarin mutuwarsa.

"Mun ji sauran firsunoni na ta bugun keji sun iwun cewa Mursi ya mutu."

Tun lokacin da aka yiwa Mursi juyin mulki a ransr 3 ga Yuli, 2013, shugaban kasar Misra, Abdel Fatah Al Sisi ya fara fito na fito yan kungiyar Ikwan inda aka jefa dubunnai cikin kurkuku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng