Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kan kai hari Borno yanzunnan

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kan kai hari Borno yanzunnan

Wasu gungun yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suna kan kai hari barikin soji Gajiram, hedkwatan karamar hukumar Nganzai da ke jihar Borno a daren Litinin domin satar makamai.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan ta'addan sun shigo garin cikin motoci tara.

Kakakin rundunar Operation lafiya dole, Kanal Ado Isa, ya tabbatar da wannan rahoto inda yace dakarun sojin sun yi arangama da yan ta'addan.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun kai farmaki barikin sojin inda suka sace manyan makamai kuma suka bankawa wasu sassan barikin wuta.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa yan Boko Haramin sun sace magunguna, kayayyakin masarufi kafin wucewa.

Har yanzu ba'a san iyakan wadanda suka rasa rayukansu ba amma an samu labarin mutum daya da ya jikkata sakamakon harbin bindiga.

Wannan harin ya faru ne kimanin sa'o'i 24 bayan harin kunar bakin wake ya hallaka akalla yan kallon kwallo 30 a garin Kanduga.

Gajiram ce hedkwatan karamar hukumar Nganzai, inda mutane daga sassan karamar hukumar ke zaman gudun hijra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng