'Da Allah na dogara' - Atiku ya yi karin bayani a kan cewar zai jagoranci zanga-zanga

'Da Allah na dogara' - Atiku ya yi karin bayani a kan cewar zai jagoranci zanga-zanga

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar a 2019, ya ce ya dogara ne da Allah.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake musanta cewar ya yi barazanar jagorantar zanga-zanga idan kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta yanke hukunci da bai yi masa dadi ba.

A wani sakon da shafin YouthSupportPDP ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya rawaito Atiku na ce wa: "sakamakon zaben da nake da shi daga na'urar hukumar INEC sahihi ne, kuma idan alkalan kotu suka yi kokarin danne min hakki, zan jagoranci zanga-zangar da za ta mamaye titunan Najeriya. Zan jagoranci 'yan Najeriya wata gagarumar zanga-zanga da ba a taba ganin irinta ba."

Sai dai dan takarar shugaban kasar ya ce alakanta shi da jawabin, "aikin masharranta ne da ke son bata masa sunansa a siyasa," tare da bayyana jawabin a matsayin zuki tamalle.

DUBA WANNAN: Wata guguwa mai karfi ta lalata gidaje fiye da 1000 a jihar Zamfara

"Ina son sanar da jama'a cewa wancan jawabi ba daga bakin Atiku ko wani nakusa da shi ya fito ba. Aiki ne na masharranta da ke son bata masa suna da kuma rataya masa laifin cewar ya zama barazana ga zaman lafiyar kasa," a cewar jawabin da Paul Ibe, kakakin Atiku, ya fitar amadadinsa.

"Ya kamata kowa ya sani cewa Atiku Abubakar mutum ne mai bin dokokin Najeriya. A shekaru fiye da 40 da ya yi yana siyasa, bai taba daukan wani mataki ko furta kalaman da suka saba wa dimokradiyya ba kuma ba zai fara ba yanzu.

"Atiku da tawagarsa sun dogara da Allah, kuma mu na kira ga masu kulla sharri da su ji tsoron Allah su canja hali. Dimokradiyya ta samu matsuguni a Najeriya. Duk wata tsoratar wa ba zata hana mu yin siyasa ba. 'Yan Najeriya na da tarihin yin tirjiyya ga zalunci da azzalumai kuma da yardar Allah zasu cigaba da yin hakan," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel