Matasa a Taraba sun far ma ofishin yan sanda, sun saki makeran bindiga 3 sannan suka yi wa yan sanda dukan tsiya

Matasa a Taraba sun far ma ofishin yan sanda, sun saki makeran bindiga 3 sannan suka yi wa yan sanda dukan tsiya

- Wasu matasa sun kai hari ofishin yan sanda a Wukari, jihar Taraba, inda suka saki makeran bindiga uku

- Jami’an tsaro na shirin mayar da masu laifin Jalingo ne lokacin da matasan suka kai mamaya ofishin sannan suka sake su

- Kakakin yan sandan jihar, DSP David Misal, yace ba a kai rahoton lamarin ga rundunar ba

Wasu matasa a garin Wukari, jihar Taraba sun far ma ofishin yan sanda a yankin sannan suka kubutar da wasu mutane uku da yan sanda suka kama kan laifin kera bindigogi.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jami’an yan sandan sun kama mutane ukun ne a garin Wukari a ranar Lahadi bisa zargin kera bindigogi daga Jalingo sannan suka kai su ofishin yan sanda don tsaro.

An tattaro cewa jami’an tsaron na shirye-shiryen tafiya da masu laifin Jalingo ne a lokacin da matasan suka far ma ofishin yan sandan sannan kuma suka kubutar da masu laifin.

Wani majiyi wanda ya ki bayyana sunan shi ga Daily Trust a ganawar wayar talho ya bayyana cewa matasan sun kai hari ofishin yan sanda, inda suka yiwa yan sandan duka sannan suka kubutar da masu laifin.

Har ila yau idan zaku tuna a 2013 ne matasan garin suka kona ofishin yan sanda da ke garin sanadiyyan rikicin addini.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga: Gwamnan Zamfara zai gana da kwararru a fannin tsaro a kasar Dubai

A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP David Misal yace ba a kai rahoton lamarin ga rundunar ba amman yayi alkawarin tuntuban ofishin hukumar na reshen Wukari don bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: