An fara bincike kan N6.7m da aka ce goggon biri ya cinye a gidan Zoo na Kano

An fara bincike kan N6.7m da aka ce goggon biri ya cinye a gidan Zoo na Kano

- Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi umurnin bincike kan batan naira miliyan 6.7 a gidan Zoo

- Gwamna Ganduje na so hukumar yaki da rashawa na jihar ta gano lamuran da ke tattare da batan kudin

- An rahoto cewa hukumar yaki da rashawar ta fada aiki gadan-gadan bayan samun umurnin

Yan kwanaki bayan labarin hadiye kudi naira miliyan 6.7 da ake zargin wani goggon biri yayi a gidan Zoo na Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje yayi umurnin bincike a lamarin.

Gwamnan ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar da tayi bincike akan lamuran da ya kai ga batan kudin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnan ya bayar da umurnin inda hakan ya sa hukumar yaki da rashawar fadawa aiki gadan-gadan.

An rahoto cewa Ganduje ya umurci hukumar da ta yi nazari sannan ta gano abunda ya haddasa zargin.

Ya kuma umurci hukumar da ta bankado komai da ke kewaye da al’amarin.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutane da dama yayinda sabon rikici ya barke a Jalingo

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an nemi cinikin bukukuwan sallah da aka yi a gidan Zoo na jihar Kano an rasa.

Gidan Rediyon Freedom na jihar Kano ya cigaba da gabatar da bincike akan yadda aka yi miliyan goma na cinikin gidan Zoo din ta yi batan dabo.

Wasu jami'an gidan Zoo din sun bayyana cewa suna zargin wani Gwaggon biri da sace miliyoyin kudaden, kuma har yanzu ba a san inda ya boye kudin ba. Sai dai kuma sun bayyana cewa suna zargin da ya sace kudin hadiyewa yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: