An kashe mutane da dama yayinda sabon rikici ya barke a Jalingo

An kashe mutane da dama yayinda sabon rikici ya barke a Jalingo

- Sabon rikici ya barke a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba

- Wasu yan bindiga da ba a san su wanene ba sun kai mamaya wani yanki na babbar birnin jihar inda suka haddasa tashin hankali a yankin

- Wani matafiyi, Mallam Musa Dauda, wanda ya tsallake rijiya da baya, yace ya ga gidaje da dama suna ci da wuta

An kasha mutane da dama sannan an kona gidaje a wani sabon rikici da ya barke a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yankunan da abun ya shafa harda Kasuwan Bera.

Wasu daliban jami’ar jihar Taraba, Jalingo, da suka tsere daga yankin, sun bayyana cewa sun ga daruruwan mutane, ciki harda mata da yara, suna tserewa daga yankin.

Wani matafiyi, Mallam Musa Dauda, wanda ya tsallake rijiya da baya, yace ya ga gidaje da dama suna ci da wuta.

Barnabas Francis, wani mazaunin Kasuwan Bera, ya fada ma SaharaReporters a wayar tarho: “Jalingo na cikin wuta. Fulani makyaya sun kai mamaya suna ta harbi ba kakkautawa. Mun tsere.

“Wasu daga cikin yan uwanmu sun tsere daga Jauro-Sabai inda aka kona gidaje da dama a yankin, sannan daga nan muna iya hango hayaki mai kauri."

Sai dai kuma, yan sandan Taraba sun gaza bayana halin da jihar ke ciki, yayinda David Misal, jami’in hulda da jama’a na yan sanda jihar, yace rundunar ta amsa kira mara dadi daga Yelwan-Tau, wani gari kusa da ATC.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake gidan kallo, akalla rayuka 20 sun salwanta

“Ba zan iya tabbatar da komai ba a yanzu, abunda na sani yanzu shine mun samu kira daga Yelwan-Tau kuma jami’anmu sun tafi yankin domin magance kalubalen tsaro a yankin.

“Don haka a yanzu, ba zan iya fadin komai game da lamarin ba ko kuma batun yawan mutane da aka kashe, dan Allah,” Inji Misal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel