Da duminsa: Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake gidan kallo, akalla rayuka 20 sun salwanta

Da duminsa: Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake gidan kallo, akalla rayuka 20 sun salwanta

- Yan kunar bakin wake sun tayar da Bam a cikin garin Konduga a jihar Borno

- Akalla mutane 30 sun jikkata yayinda kimanin 20 suka hallaka

- An damke daya daga cikin maharan

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu yayinda kimanin 30 suka jikkata sakamakon mumunan harin kunar bakin wake da yan Boko Haram suka kai wani gidan kallo garin Konduga dake jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan harin ya faru ne ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2019.

Wani majiyar gidan soja wanda ya laburtawa Sahara Reporters ya ce yan kunar bakin wake biyu, namiji da namace, sun tayar da Bam a gidan kallon dake unguwar Mandarari dake karamar hukumar Konduga misalin karfe 9:15 na dare.

Bayan haka, an damke wata yar kunar bakin baki wacce Bam dinta yaki tashi kuma an mikata ga hukumar sojin Najeriya.

Majiya ta bayyana cewa kawo yanzu, an kirga gawawwaki 17, wanda ya hada da wani jami'in dan sanda.

Wani jami'in hukumar kato da gora wanda aka sakaye sunansa yace: "Labarin ya bayyana cewa yan kunar bakin wake uku, mata 2 da namiji 1 suka tayar da Bam, sun kashe kansu da kuma wadanda ke gidan kallon da wani dandali a Mandarari."

"Duk da cewan mutane 17, hada da wani dan sanda suka mutu, wadanda suka jikkata sun kai 30."

A lokacin da muke kawo wannan rahoto, hukumar soji da na yan sanda basu yi wani jawabi a kai ba domin sanin irin barnar da akayi. Amma wasu jami'an hukumar kawo agaji na gaggawa wato SEMA sun tabbatar da yawan wadanda abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng