Wani matashi ya mutu bayan ya saci wani gunki da 'yan kabilar Tiv ke bauta wa a Wukari

Wani matashi ya mutu bayan ya saci wani gunki da 'yan kabilar Tiv ke bauta wa a Wukari

Wani mutum mai matasakaicin shekaru ya mutu kwana uku kacal bayan ya sace wani gunki daga wata shekar tsafi da ke wani garin 'yan kabilar Tiv a jihar Taraba.

Matashin, kamar yadda rahotanni suka bayyana, tare da wasu matasa sun dira garin da ke karamar hukumar Wukari domin lalata dukiyoyin jama'a a rikicin da ke cigaba da gudana a tsakanin 'yan kabilar Tiv da Jukun.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar matashin ya saci gunkin, kuma ya tafi da shi dakinsa ya boye ba tare da ya sanar da ragowar abokansa da suke tare ba.

Wani mutum, Shamaki Solomon, ya shaida wa Daily Trust cewar matashin ya kasa yin bacci a ranar da ya sato gunkin.

Majiyar ta bayyana cewar 'yan kabilar Tiv da ke kauyen da aka sato gunkin, sun dogara da shi domin samun kariya.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Gaskiyar abinda yasa Buhari ya rabu da matarsa ta farko, Safinatu

Solomon ya kara da cewa kafin matashin ya mutu, ya bayyana cewar ya ji wata kara daga kusurwar da ya ajiye gunkin a dakinsa tare da jin wata katuwar murya na cewa 'ina bukatar jinin da zan sha'.

Majiyar ta kara da cewa tun da matashin ya ji muryar ya kasa bacci har na tsawon kwana uku kafin daga bisani ya kamu da rashin lafiyar da ta zama silar mutuwar sa.

A kan yadda suka yi da gunkin, Solomon ya bayyana cewar kowa na jin taba gunkin da matashin ya boye a cikin wata jaka a dakinsa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce ba a sanar da rundunar 'yan sanda faruwar lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel