Matar gwamnanan APC ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa

Matar gwamnanan APC ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa

- Amina Bello, matar gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa

- Besty Obaseki, matar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ce ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin kudu

- Dukkan matan na auren gwamonin da suka ci zabe a karkashin tutar inuwar jam'iyyar APC ne

An tabbatar da matar gwamnan jihar Neja, Amina Bello, a matsayin shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa.

A sanrwar da sakatariyar yada labarai, Aisha Wakaso, ta sa hannu a kai, ta ce kungiyar matan gwamnonin sun amince da nada Amina a matsayin sabuwar shugabar kungiyar a taron da suka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.

Wakaso ta bayyana cewar an nada Amina a mukamin ne bayan mijin tsohuwar shugabar kungiyar ya fadi zaben 2019.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci: Baraka na kokarin kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu

Hadiza Abubakar, matar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ce ta]sohuwar shugabar kungiyar matar gwamnonin arewa.

Besty Obaseki, matar gwamnan jihae Edo, Godwin Obaseki, ce ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin kudu.

Besty ta karbi shugabancin kungiyar ne daga hannun Nkechi Okorocha, matar tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel