Matakin Nasara: Jamiyyu 10 sunyi Mubaya'a ga Matawalle

Matakin Nasara: Jamiyyu 10 sunyi Mubaya'a ga Matawalle

-Jam'iyyun siyaysa guda 10 a jihar Zamfara sun janye hannunsu daga tuhumar da dan takarar Gwamna na jam'yyar APP ke yiwa Matawalle

-Dan Karar gwamna na jam'iyyar APP ya shigar da karar ne a kotun zabe dake Abuja inda kuma ya ce yana kalubalantar Matawalle tare da goyan baya jam'iyyu 10 a jihar

-Shuwagabannin jam'iyyun sunyi kira ga al'ummar jihar da su yi mubaya'a ga sabuwar gwamnatin kuma su taya ta da addu'a

Jam'iyyun siyasa guda 10 a jihar Zamfara sun ce babu hannunsu a kalubalantar da ake yima Matawalle a kotu na nasararsa zama gwamnan jihar wanda jam'iyyar APP ta ce ta shigar.

Kamfanin dillacin labaai na Najeriya ya ruwaito cewa dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APP, Alhaji Zayyanu Haske, ya shigar da kara a kotun zabe dake Abuja.

Haske na rokon kotun da ta soke zaben da ya kawo Matawalle a matsayin gwamnan jihar.

Dan takarar na jam'iyyar APP na ikirarin cewa da goyan bayan wasu jam'iyyu a jihar ya shigar da karar.

KARANTA WANNAN: Buhari ya umurci CBN da su sa ido akan masu shigowa da Manja

A lokacin da suke mayar da martani, shuwagabannnin jam'iyyu guda 10, karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), Alhaji Musa Mai-mai, sunce babu ruwansu a cikin karar kuma ba wanda yayi shawara dasu a lokacin da ya aka shigar da karar.

"Ba ayi shawara da mu ba, mun yarda da hukuncin da kotun koli ta Najeriya tayi, wanda ta soke zaben fidda gwani na jam'iyyar APC wanda sanadiyyar hakan ne Matawalle ya zama gwamna."

A lokacin da yake ganawa da yan Jarida a Gusau, Shugaban jam'iyyar ta AD Alhaji musa, ya ce wadanda ke kalubalantar Matawalle na "yin adawa marar kan gado wanda hakan ba dai dai bane."

"Mu babu ruwanmu a tafiyarsu, muna so duniya ta sani cewa su kadai ke tafiyarsu"

Ya kara da cewa "Mafi yawan shuwagabanni da dattawan jihar nan sunyi mubaya'a ga sabuwar gwamnatin ciki ko hadda tsohon gwamna Abdul Aziz Yari. A sabida haka muna tunanin zasu bi wannan gwamnati za kuma su taimaka mata wajen ganin ta cimma nasara."

Shugaban na jam'iyyar AD yayi kira ga al'ummar jihar da su yi biyayya ga gwamnatin su kuma taya ta da addu'a don ganin cewa tayi nasara musamman wajen magance matsalolin tsaro.

Sauran jam'iyyun da suka janye hannunsu daga tuhumar da ake ma Matawalle sun hada da PRP, SDP, ID, HD, ASD, MMN, NAC, KOWA da kuma FRESH.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng