Da izinin majalisar shari'a a Abuja na nada sabon alkalin alkalai - Gwamna Atiku Bagudu

Da izinin majalisar shari'a a Abuja na nada sabon alkalin alkalai - Gwamna Atiku Bagudu

- Daga karshe, gwamnan jihar Kebbi ya sallami Alkali Asaba

- Mai shari'a Asabe Karatu ta zargi gwamna Bagudu da nuna bangarancin addini

- Gwamnan ya yi fashin baki kan abinda ya hana tabbatar da ita

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a ranar Juma'a ya rantsar da Alkali Mohammed Sulaiman Ambursa a matsayin sabon mukadddashin alkalin alkalan jihar sakamakon rashin amincewar majalisar dokokin jihar da alkali Asabe Karatu.

Ya yi karin haske kan jita-jitan da ke yawo cewa an ki tabbatar da Asabe Karatu ne saboda addininta, ya ce dalilin da hana tabbatar da ita shine zargin da ake yi mata na mallakan takardun bogi.

Ya ce an samu matsala wajen ranar haihuwanta dake kan takardar shaidan kammala karatun firamare daga 1952 zuwa 1954 kuma yan majalisan sun lashi takobin cewa ba zasu tabbatar da ita ba duk da nacewar gwamnan.

Da izinin majalisar shari'a a Abuja na nada sabon alkalin alkalai - Gwamna Atiku Bagudu

Da izinin majalisar shari'a a Abuja na nada sabon alkalin alkalai - Gwamna Atiku Bagudu
Source: Facebook

Gwamnan ya kara da cewa ya yanke shawaran nada alkali Sulaiman Ambursa matsayin mukaddashin alkalin alkalan jihar bisa ga shawara majalisar shari'a wacce ya rubutawa wasika kuma suka turo tawagar alkalai karkashin jagorancin babban alkalin Abuja, Isiaku Bello.

Bayan ganawarsu, sun bashi shawarar cewa ya nada wani alkali mafi girma a jihar kuma Alkali Sulaiman Ambursa ne.

An haifi Ambursa a ranar 25 ga Disamban 1957 kuma ya halarci jami'ar Usmau Dan Fodi a jihar Sokoto inda ya yanki tutar zakarar shekara.

Ya karantar a makarantun firamare da sakandare kafin komawa bangaren shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel