Talauci ne ke kawo tashin hankali a kasarmu, inji Buhari

Talauci ne ke kawo tashin hankali a kasarmu, inji Buhari

-Shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa kasar Najeriya zata iya tsamo mutum miliyan 100 daga cikin kangin talauci a shekara 10, yayin da yake gabatar da jawabin ranar dimokuradiyya.

-Sai dai wani masanin tattalin arziki na ganin hakan ba abu bane mai yiwuwa, saboda a cewarsa babu wani tsari da ake a yanzu wanda zai bada tabbacin cewa gwamnati ta shirya aiwatar da abinda ta fadi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin talauci da tashe-tashen hankula dake addabar Najeriya a halin yanzu.

Shugaban wanda ke jawabi a ranar bikin cika shekara 20 na kawo karshen mulkin soji a Najeriya ya ce: “ Idan banbanci tsakanin masu kudi da talakawa ya karu, to sai rashin zaman lafiya ma ya karu.”

KARANTA WANNAN:Jawabin Buhari cike yake karyar abubuwan da ba’ayi ba – PDP

Ya kara da cewa: “ Tabbas zamu iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci a cikin shekara 10 idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata.”

Shugaba Buhari wanda ya fara wa’adi na biyu ranar 29 ga watan Mayu, an zabe shi ne bisa alkawarin samar da yaki da cin hanci da rashawa.

Sai dai kuma a daidai lokacin da aka samu raguwar hare-haren Boko Haram, an samu karuwar sace-sacen jama’a da kuma hare-haren yan bindiga a sassa daban-daban na kasar nan.

Bugu da kari, shugaban ya cigaba da cewa: “ Tunda kasashen China da India suka cigaba babu abinda zai hana Najeriya ma cigaba.”

Sai dai bai yi cikakken bayanin yadda zai yi hakan ba, abinda ya sanya wani masanin tattalin arziki mai suna Abubakar Aliyu ke ganin zance ne kawai wannan magana ba komi ba, kamar yadda ya sahidawa BBC.

Abubakar ya ce: “A yanzu haka babu tsari da ake da shi a kasa wanda zai nuna hakan mai yiwuwa ne, a don haka ni ina ganin kalamai ne kawai na dadin baki kamar yadda ‘yan siyasa suka saba yi.”

Najeriya ce kasar da tafi ko wacce kasar Afirka yawan jama’a da kuma arzikin man fetur, amma duk da haka tana gaba cikin kasashen dake fama da rashin cigaba wanda ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel