Gwamnatin Niger zata siyo tarakatoci akan Kudi Naira biliyan 1.8

Gwamnatin Niger zata siyo tarakatoci akan Kudi Naira biliyan 1.8

- Gwamnatin Niger ta shirya ta tsaf don siyo tarakatoci 10 akan kudi Naira biliyan 1.8 don habbaka aikin gona na bana.

-Gwamnatin Niger ta kaddamar da rabon taki da kayan aikin gona

Gwamna Abubakar Bello ya bayyana cewa sun shirya tsaf don siyo tarakatoci 10 akan kudi Naira biliyan 1.8 a Minna babban birnin jihar Niger a lokacin da yake kaddamar da rabon taki, iri da sinadaran aikin gona ga manoma.

"Don kara yawan tarakatoci a wannan jihar, zamu siyo tarakatoci 10 akan kudi Naira biliya 1.8 "

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Ahmed Ketso, ya ce gwamnatin jihar tayi hadaka da wasu masu ruwa da tsaki akan harkar noma don tabbar da shirin.

KARANTA WANNAN: Likafa ta cigaba: An nada Sarkin Kano wani muhimmin mukami a yankin yarbawa

Gwamnan ya kara da cewa za a siyar da takin, irin, da sinadaran aikin noma ga manoman da gwamnati ta tantance akan kudin Naira 5,500 kamar yadda gwamnatin tarayya ta kayyaje

"Za a saukar da takin a wajajen da gwamnati ta tantance na adana taki a kananan hukumomi 25 a fadin jiharnan don siyarwa ga manoma akan kudi Naira 5,500."

Gwamnan ya bayyana cewa cikin kayayyakin da za a kawo sun hada tan 8,000 na irin shinkafa, tan 5,000 na irin masara da kuma tan 5,000 na irin dawa.

Sauran kayayyakin sun hada da tan 3,000 na waken soya da kuma lita 16,000 ta maganin ciyayi.

Tun farko babban sakataren ma'aikatar noma da ci gaban kauyuka Ibrahim Musa ya yi kira ga manoman da su kauracewa siyan gurbataccen taki da sauran kayayyakin noma.

.Musa yayi jinjina akan yadda aka siyar da kayan aikin cikin lokaci saboda hakan zai bunkasa albarkar noma a jihar.

Haka zalika shugaban kungiyar manoma ta jihar Shehu Galadima ya godewa gwamnatin akan taimakon da tayi cikin lokaci.

Galadima ya bukaci gwamnati da ta dauki mataki don magance matsalolin tsaro a jihar don kariyar manoman.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel