Zamfara: Duk sarkin da ya bari aka kashe mutum a masarautarsa zan tsige shi - Matawalle

Zamfara: Duk sarkin da ya bari aka kashe mutum a masarautarsa zan tsige shi - Matawalle

- Gwamnan jihar Zamfara yayi alkawarin tumbuke duk wani sarki da ya sake bari aka zubar da jinin mutane a masarautarsa

- Gwamnan yayi bayanin ne jiya a lokacin da ake bikin ranar Demokradiyya a garin Gusau

- Sannan yayi alkawarin samar da sana'o'i da ayyukan yi ga matasan jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya sha alwashin cire duk wani sarki da ya bari 'yan bindiga suka kashe mutum a masarautarsa.

Yayi bayanin hakanne a jiya yayin da yake jawabi lokacin bikin ranar Demokradiyya da aka gabatar a garin Gusau babban birnin jihar.

Daga nan gwamnan ya bai wa sarakunan gargajiyar damar ganawa da 'yan kungiyar sa kai da kuma 'yan banga domin gargadinsu akan kisan mutane a kasuwanni. Idan ba haka ba kuma rawunansu zasu dinga sauka. Sannan kuma yayi alkawarin kashe duk mutumin da aka kama da hannu a kisan wani.

Gwamnan ya kuma jadadda jawabin sa na cewa gwamnatinsa za ta tafi da duk masu son kawo cigaba ga al'ummar jihar ba tare da bambancin siyasa ko jam'iyya ba.

KU KARANTA: Yadda Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani zagi saboda ya kirata da tsohuwa

Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar akan cewa kowannensu yana da gudumawar da zai bayar ta bangaren tsaro a jihar. Sannan kuma ya sake kira ga 'yan jihar da suke zaune a wasu sassa na kasar nan da kuma kasashe na duniya, da cewa kofa a bude take ga duk wani wanda zai bada gudumawa domin samar da tsaro a jihar.

Matawalle yayi alkawarin samar da sana'o'i, sannan kuma ya bada umarnin tada duk wasu masana'antu na jihar domin su fara aiki. Ya kara da cewa zancen bangar siyasa da yawon maula da matasa ke yi ya kare a jihar Zamfara.

Gwamnan jihar, ya bayar da umarnin tada kamfanin takin zamani wanda yake mallakar jihar, inda ya kara da cewa daga yanzu duk wani taki da manoman jihar zasu yi amfani dashi, a cikin jihar za a samar dashi.

A jawabin da yayi, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Mallaha ya bayyana cewa, wannan rana rana cewa ta samun 'yancin kai a siyasa.

"Rana ce ta alfahari a garemu mu 'yan jam'iyyar PDP a jihar nan da muke da gwamna, 'yan majalisun tarayya dana jiha duka 'yan jam'iyyar PDP, dan haka muna godiya ga Allah da irin wannan ni'ima da yayi mana," in ji shugaban jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel