2019: Sanata Shehu Sani ya maidawa El-Rufai dogon martani a Facebook

2019: Sanata Shehu Sani ya maidawa El-Rufai dogon martani a Facebook

A cikin makon nan ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fito ya na ikirarin cewa ya yi wa Sanatocin jihar; Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi ritaya a siyasa. Tuni Shehu Sani ya fito ya maida masa martani.

A Ranar Talata, 11 ga Watan Yunin 2019, tsohon Sanatan Kaduna-ta-tsakiya, Shehu Sani ya yi amfani da shafin sa na Facebook yayi wa Gwamnan raddi a game da maganganun da yayi ta manhajar yanar gizo ba da dadewa ba.

1. Ba za ka ce ka yi wa wani ritaya daga siyasa ba don kurum ka zage da makalewa a bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ka na kai masa tsegumi.

2. Ba za ka iya tsayawa da sunan ka, ka nuna irin karfin ka a siyasa ba tukuna har yau, Ko da ka nemi kayi takarar Gwamnan Gwamnoni kwanan nan, kashi ka sha.

3. Ka na da mummunan tarihin canza Uban-gida kamar yadda kowa ya sani a Najeriya, kuma kwanan nan za ka rabu da Buhari da zarar ka samu abin da ka ke so.

4. Ba a kan ka ne a ka fara yin tazarce a jihar Kaduna ba, Makarfi da yayi shekaru 8 a mulki, bai taba cewa yayi wa wani ritaya ba, kuma ba a shiga kotun zabe da shi ba.

5. Babu mamaki don ka dawo ka na cewa ka yi mana ritaya, bayan ka shafe dare da rana ka na rokon Buhari da Oshiomhole a ba ka dama ka canza Sanatocin Kaduna.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya sake caccakar Saraki da Dogara

(Kowa a ofishin Oshiomhole ya san yadda ka rika zarya babu dare-babu rana, ka na tsugunawa, ka kuma yi wa Buhari kuka saboda a kyale ka, ka nada wanda ka ke so a Sanatan Kaduna)

6. A cikin shekaru 4 da su ka wuce, an ta kawo mani farmaki iri-iri a jihar Kaduna, wanda manufar su ba boyayye ba ne. Ka ma taba fitowa ka na kiran mutane su hallaka ni a 2018.

7. Giyar mulki ta na dibar ka, amma kamar yadda na saba fadi, ba a dawwama a kan mulki komai dadewa a kan karaga, wata rana za ka koma daga kai sai halinka.

8. Za ka iya cigaba da labewa ka na cin albarkacin Buhari, ko ka yi amfani da karfin mulki ka na so a kashe ni da Sanata Hunkuyi, amma ba ka isa ka sa mu yi tsit ba.

9. Ka daina huce takaicin ka a kai na.

10. Iyalin ka da ‘Ya ‘yan ka ba su da abin magana sai mu, ka shafa mani lafiya mana.

11. Ina alfahari da kuri’un da na samu a zabe ba tare da raba kan al’umma ko likewa shugaba Buhari ba.

12. Kafin in bar APC na fadawa shugaba Buhari, Oshiomhole da Tinubu cewa wata rana za ka zage su, ka yaudare su, ka kuma yi fada da su. Wannan a jinin ka yake.

13. Giyar mulki ya dauke ka, har yanzu zuciyarka ba ta natsu ba, idan ba haka ba, mai zai sa ka rika kiran Shehu Sani, bayan ka masa ritaya a siyasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel