APGA zata kalubalanci Matawalle a matsayin gwamnan Zamfara

APGA zata kalubalanci Matawalle a matsayin gwamnan Zamfara

Jam’iyyar APGA tace zata kalubalanci Bello Matawalle na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar 9, Maris 2019 a jihar Zamfara.

Hakan ya biyo bayan da jam’iyyar da dan takararta Dr. Sani Abdullahi Shinkafi suka janye tuhumar da suke yi game da bayyana dan takarar APC a matsayin gwamnan jihar Zamfara.

Bayan da suka janye karar, lauyan Shinkafi da Jam’iyyar, Ifeanyi Mbaeri ya bayyana cewa suna duba yiyuwar tuhumar bayyana Bello Matawalle a matsayin zababben gwamna da hukumar INEC tayi, saboda bai cancanci ya tsaya takara ba.

A cewar Mbaeri "mun janye tuhumar da Dr. Sani Abdullahi shinkafi da APGA suka yi inda suke kalubalantar bayyana APC da dan takararta a matsayin wayanda suka lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar 9 Maris 2019.

"Wannan ya biyo bayan hukuncin da kotun koli tayi ranar 24 Mayu 2019 inda ta soke zaben dukkan yan takarar APC na zamfara bisa dalilin rashin yin ingantaccen zaben fidda gwani."

KARANTA: Fara wa da zafi-zafi: Gbajabiamila ya nada Sanusi a matsayin shugaban ma'aikatansa

Kotun kolin ta zartar da hukunci wanda Mai shari’a Adamu Galunje ya karanta, kotun ta amince da hukunci kotun daukaka kara ta yankin Sokoto, inda ta amince cewa jam’iyyar bata gudanar da ingantaccen zaben fidda gwani ba, a cewarshi “ baya yiyuwa a ce jamiyyar da bata da dan takara taci zabe , a sabida haka kuriun da APC ta samu baza ayi amfani da ita ba”

A sabi da haka, kotun wacce alkalai biyar suka gudanar da ita karkashin mukadasshin alkalin alkalan Najeriya Tanko Muhammad ta tabbatar da jam’iyyar da ta yi na biyu wajen yawan kuri’u a matsayin wadda ta lashe zaben.

INEC ta yi biyayya ga hukuncin kotun kolin inda ta bayyana dan takarar PDP Matawalle a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar zamfara.

Mbaeri ya bayyana cewa “ akwai yiyuwar wanda nike wakilta, Shinkafi da APGA su kalubalanci matawalle a matsayin gwamnan Zamfara, kuma suna duba yiyuwar shigar da kara a kotun zabe don kalubalantar matsayar INEC na Bayyana Matawalle a matsayin gwamnan zamfara.”

har yanzu muna cikin kayyajajjen kwana 21 na shigar da korafin zabe, kuma APGA da dan takararta na duba yiwuwar kalubalantar Matawalle da PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a 9 Maris, dogaro da sashe na 143 na dokokin Zabe 2010 da kuma sashe na 177 na kundin tsarin mulkin Najeria.

Mbaeri ya bayyana cewa Dokokin zabe da kundin tsarin mulki na Najeriya ya zayyana wasu sharudda da dole kowanne dan takara zai cika, kuma suna da yakinin cewa dan takarar PDP Matawalle bayada cikakkun takardun makaranta.

A bisa wannan dalilin ne zasu kalubalancin Matawalle akan cewa bai can canta ba tunda bashi da takardun karatu kamar yadda kundin tsari mulki ya tanadar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel