Sabon gwamnan jahar Yobe ya raba ma talakawa gidan sauro guda 2,300,000

Sabon gwamnan jahar Yobe ya raba ma talakawa gidan sauro guda 2,300,000

Sabon gwamnan jahar Yobe, kuma tsohon sakataren jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya kaddamar da rabon gidajen sauro domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da suka kai guda miliyan biyu da digo uku (2,300,000).

Jaridar Blue Print ta ruwaito gwamnatin jahar Yobe ta kaddamar da aikin rabon gidajen sauron ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya, da wasu hukumomi masu rajin samar da cigaba.

KU KARANTA: Masu uwa a gindin murhu: Yaron tsohon gwamna, kuma Sanata a yanzu ya zama kaakakin majalisa

Da yake kaddamar da aikin rabon gidajen sauron a fadar Sarkin Damaturu, gwamnan jahar Yobe, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Idi Barde Gubana yace manufar aikin rabon gidajen sauron shine kare jama’a daga sharrin cizon sauro.

“Mun kaddamar da wannan aiki ne domin hanzartar yunkurin gwamnatin tarayya na kawar da cutar zazzabin cizon sauro daga Najeriya gaba daya, musamman duba da manufar gwamnatinmu na bada fifiko ga kiwon lafiya a jahar Yobe.

“Haka zalika muna da manufar samar da dakin shan magani da karbar haihuwa akalla guda daya a kowacce mazaba dake cikin kananan hukumomin jahar Yobe, tare da fadada aikin rigakafin cutar shan inna.” Inji mataimakin gwamna Idi.

Alhaji idi ya yi kira ga sarakunan gargajiya dasu taimaka wajen wayar da kan jama’a tare da kokarin ganin kowa ya samu wannan gidan sauro a kafatanin kananan hukumomin jahar guda 17.

Daga karshe shugaban hukumar kiwon lafiya ta jahar Yobe, Muhammad Lawan ya bayyana godiyar gwamnatin jahar ga hukumomin da suka bada goyon bayan wajen samar da gidajen sauron, sa’annan ya gargadi jama’a da kada su sayar da gidajen sauron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel