'Yan sanda sun cafke mutane 55 da suke da hannu a kisan mutum 1 da raunata 14 a jihar Bauchi

'Yan sanda sun cafke mutane 55 da suke da hannu a kisan mutum 1 da raunata 14 a jihar Bauchi

- An kama mutane 55 da ake tunanin suna da hannu a tada zaune tsaye a jihar Bauchi

- Mutanen ana zargin sune suka tada fitinar da tayi sanadiyyar mutuwar wani mutumi da kuma raunata mutane da dama a jihar Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar cafke mutane 55 da ake zargin suna da hannu a rikicin taho mu gama da ya faru a jihar Bauchi.

Rikicin ya faru jiya Laraba da yamma a cikin garin Bauchi a lokacin da ake gabatar da Hawan Daushe.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Kamal Datti Abubakar, shine ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar kama mutanen kuma ta kwace makamai a hannunsu.

Ya bayyana cewa rikicin ya faru a lokacin hawan salla, lokacin da Hakiman masarautar Bauchi suke kai gaisuwa ga gwamnan jihar, Bala Mohammed Kaura a gidan gwamnatin jihar.

"A lokacin ne, kungiyar mafarauta da suke bin Hakimin Darazo da kungiyar dake bin Hakimin Duguri suka fara rikicin, a sakamakon rikicin wani mutumi mai suna Auwalu Sadau dake karamar hukumar Darazau ya rasa ransa, bayan ya samu rauni sakamakon wani harbin bindiga da aka yi. Yayin da Usama Musa dake garin Duguri, cikin karamar hukumar Alkaleri da Zakari Suleiman daga karamar hukumar Darazo tare da wasu mutane 12 suka samu raunika, yanzu haka dai suna karbar magani a asibitin koyarwa na ATBU," in ji shi.

KU KARANTA: Wani mutumi yayi wa matarsa dukan kawo wuka saboda tayi masa wata tambaya akan karuwarshi

Ya kara da cewa cikin gaggawa rundunar 'yan sandan jihar da hadin gwiwar rundunar sojin 'Operation Puff Adder' suka kai dauki gurin inda suka kama mutane 55, yanzu dai kura ta lafa a garin.

A cewar mai magana da yawun hukumar, an samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske, wadanda suka hada da adduna, wukake, gario, sanduna da sauransu.

Ya kara da cewa yanzu haka dai suna nan suna cigaba da bincike akan lamarin.

Haka kuma gwamnan jihar, Bala Mohammed Kaura ya kaiwa wadanda suka ji rauni ziyara a asibitin da suke karbar maganin, sannan yayi kira ga al'umma su zauna lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel