Buhari yayi sallar idi a masallacin sansanin Mabilla da ke Abuja (hotuna)

Buhari yayi sallar idi a masallacin sansanin Mabilla da ke Abuja (hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci sallar Eid El Filtri a masallacin idi na sansanin Mabilla da ke Abuja a ranar Talata, 4 ga watan Yuni.

Daga cikin wadanda suka halarci masallacin tare da Shugaban kasar sun hada da Shugaban hafsan sojoji Tukur Yusuf Buratai, Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Frmi Gbajabiamilla, Sanata Kabiru Gaya da kuma Shugaban rundunar yan sandan Najeriya Adamu Mohammed.

Babban limamin sojoji, Kyaftin Yusuf ne ya jagoranci sallar idi a masallacin.

Buhari yayi sallar idi a masallacin sansanin Mabilla da ke Abuja (hotuna)

Buhari yayi sallar idi a masallacin sansanin Mabilla da ke Abuja
Source: Twitter

A ranar yau Talata ne dai daukacin al'umman Musulmi ke bikin karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadana na tsawon kwanaki 29.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari a jiya Litinin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da halayyar da suka kasance akai cikin watan Ramadana.

Ya kuma nuna farin cikinsa bisa gudanar da zabe da akayi a kasar cikin kwanciyar hankali da lumuna, duk da cewa anyita hasashen za’a samu tashin hankali lokacin zaben.

KU KARANTA KUMA: Bikin karamar sallah: Hukumar yan sanda ta sanar da hana zirga-zirga a Borno

A sakonsa na goron sallah shugaba Buhari ya yabawa hukumar zabe bisa kokarinta na shirya zabe mai inganci a kasar nan. Kana kuma ya jinjinama ‘yan Najeriya a kan juriya da kuma nuna amincewarsu ga da abinda ake kira dimokuradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel