Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)

Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)

Sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya jagoranci ayarin jami’an rundunonin tsaro inda suka fantsama cikin dazukan kauyen Wonaka dake garin Gusau da nufin farautar miyagun yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin.

Kaakakin gwamnan, Yusuf Idris ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, inda yace gwamnan ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jahar, Mahadi Aliyu Gusau, da sauran kwamandojin rundunar tsaro, inda suka fatattaki yan bindigan.

Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)
Mutawalle
Asali: Facebook

KU KARANTA: Daga zuwa biyan kudin fansa, yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin gwamnan Katsina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan yayi wannan jarumta ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kauyen Lilo da nufin zuwa yin gaisuwar ta’aziyya bisa wani hari da aka kai ma jama’an yankin, inda aka kashe mutane 8, tare da jikkata wasu 18.

Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)
Mutawalle
Asali: Facebook

“Hangen tawagar gwamnan keda wuya yan bindigan suka fice daga mafakarsu, suka tsallake wani dan kogi dake tsakaninsu, suka ranta ana kare don tserema harbe harben jami’an tsaro dake tare da gwamnan.

“Duk da haka sai da gwamnan ya karasa garin Lilo inda yayi gaisuwar ta’aziyyar, tare da fadin a matsayinsa na babban mai tsaron jahar Zamfara, dolene na nuna shugabanci nagari, don haka bani da wani zabe face jagorantar jami’an tsaro don kaddamar da wannan hari.” Inji shi.

Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)
Mutawalle
Asali: Facebook

Matsalar tsaro a jahar Zamfara tayi Kamari, inda zuwa yanzu ta sabbaba asarar rayukan mutane fiye da 3,000, kamar yadda tsohon sakataren gwamnatin jahar, Abdullahi Shinkafi ya bayyana a shekarar data gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel