Ranar yaki da taba: Dalilai 7 da yasa ya kamata mutane su daina shan sigari

Ranar yaki da taba: Dalilai 7 da yasa ya kamata mutane su daina shan sigari

Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana sigari a matsayin annoba kuma daya daga cikin cututtukan da duniya ba ta taba ganin irinsu ba.

Ta shawarci kasashe da su dauki sabbin matakan hana amfani da taba sigari da kuma dakile tallace-tallacen da kamfanoni masu yin sigari ke daukar nauyi da ma saka haraji mai yawa.

Ta ce amfani da tobacco yana raguwa: kashi 20% na mutanen duniya ne suke shan ganyen taba sigari a 2016 idan aka kwatanta da kashi 27% a shekarar 2000.

Sai dai wannan alkaluman sun yi kadan yayin da ake kokarin bin jadawalin abin da al'ummar duniya ta amince da shi.

Ga wasu daga cikin illolin da sigari ke yiwa mai shan sa:

1. Shan sigari na haddasa mutuwar mutane miliyan shida a kowace shekara.

2. Sigari sine abu na biyu a ke haddasa mutuw sannan abu na hudu da ke haddasa cututtuka a fadin duniya.

3.Sigari na da sinadaran kemikal sama da 7,000 a hayakinsa. Akalla guda 250 na da illa, daga cikin wdannan 69 na hafar da cutar kansa.

4. Sigari na da illa ga garkuwan jikin dan Adam.

KU KARANT KUMA: Yan sanda sun gano kokon kan wani magidanci a cikin motarsa

5. Sigari ne sanadiyar munanan cututtuka sama da 25 da sukahada da hawa jini, ciwon zuciya, kansa, asma, rubewar hakora, rashin aihuwa, gyambon ciki da sauransu.

6. Sigari na haifar da matsaloli ga masu juna biyu.

7. Shan sigari na kawo kansar makokwaro

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel