Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban filin jirgin saman Sarki AbdulAziz dake garin Jiddah, kasar Saudiyya misalin karfe 6 na yammacin Alhamis, 30 ga watan Mayu, 2019.

Shugaba Buhari ya koma kasar Saudiyya bayan kimanin mako daya da dawowa daga kasa mai tsarki inda ya gabatar da ibadar Umrah sakamakon gayyatar mai martaba sarkin Saudiyya, Sarki Salman.

A birnin Makkah, Buhari zai halarci taron kungiyar kasashen Musulunci wato Organization of Islamic Co-operation, wanda ya tattara shugabannin kasashen Musulmai domin tattaunawa kan jin dadin mabiya addinin Islama a fadin duniya.

Ya samu kyakkyawan tarba daga manyan jami'an kasar Saudiyya karkashin jagorancin mataimakin gwamnan birnin Makkah, Yarima Abdullah bin Bandar bin AbdulAziz.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah
Asali: Facebook

KU KARANTA: Najeriya ta kashe N11trn wurin biyan tallafin man fetur a shekara 6 –inji majalisa

Daga cikin wadanda suka raka Buhari sune gwamnonin jihar Osun, Gboyega Oyetola; gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello; gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Talamiz; da shugaban hukumar NITDA, Sheik Dakta Isa Ibrahim Ali Fantami.

Za'a fara taron ranar Juma'a ne inda Buhari zai yi magana kan yaki da ta'addanci musamman yankin tafkin Chadi.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya yi bayanin cewa sabanin abinda wasu ke tunani cewa kungiyar OIC domin daurawa mutane Musulunci ne, tamkar wata karamar majalisar dinkin duniya.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Jiddah
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel