Seyi Makinde ya sauke shugabannin kananan hukumomin Oyo

Seyi Makinde ya sauke shugabannin kananan hukumomin Oyo

Sabon gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tsige duka shugabannin kananan hukumomin jihar Oyo daga hawansa kan mulki. Mun samu wannan labari ne ta bakin Cif Bisi Ilaka a jiya Laraba.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnan na jihar Oyo watau Bisa Ilaka, shi ne ya fitar da wannan jawabi a Ranar 29 ga Watan Mayun nan na 2019, jim kadan da rantsar da sabon gwamnan na PDP.

Ilaka yake cewa gwamnan ya kuma sauke duk wasu shugabannin mazabu na LCDA da ke jihar Oyo. Bugu-da-kari, sabon gwamnatin jihar Oyo ta ruguza duk wasu shugabannin hukumomi.

KU KARANTA: 'Yan takaran APC 5 su na neman a tsige sabon gwamna

Seyi Makinde ya sauke shugabannin kananan hukumomin Oyo

Shugabannin kananan hukumomi za su yi ta, ta kare da Makinde
Source: UGC

Daga yanzu, gwamnatin jihar Oyo ta wargaza shugabannin majalisar da ke kula da hukumomin jihar. Masu rike da mukaman shugabannin kananan hukumomin za su mikawa Darektoci aikin su.

Bayan haka, sanarwar ta nuna cewa gwamna Mai girma Seyi Makinde ya sanya takunkumi a asusun gwamnatin jihar Oyo da kuma na kananan hukumomin jihar har sai zuwa wani lokaci nan gaba.

Sai dai ma’aikatan kananan hukumomin jihar ta bakin kungiyar ALGON ta reshen jihar Oyo sun yi watsi da wannan matakin gaggawa da su kace ya sabawa doka don haka su ka nemi a tafi gaban kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel