Sa'a 1 kacal jaririyar ki za tayi a duniya - Likitoci sun shaidawa wata Mata bayan ta sauka

Sa'a 1 kacal jaririyar ki za tayi a duniya - Likitoci sun shaidawa wata Mata bayan ta sauka

A bisa al'adar rayuwa da kuma hasashe na kwararrun likitoci, ana sa ran dorewar rayuwar jarirai da suka kai kimanin nauyin kilo 2.4 zuwa kilo 3.9 yayin haihuwar su.

Sai dai hakan ba ta kasance ba ga wata jaririya da ake ikirarin cewa ita ce jaririya mafi kankanta a fadin duniya da ta ci gaba da samun dorewar rayuwa bayan haihuwar ta da nauyin da bai kai ko da na dan itaciyar Tufa daya ba.

Lamari na Mai Duka ya sanya aka haifi jaririya Saybie da nauyin da bai kai ko da na rabin kilo daya ba bayan da mahaifiyarta ta sauka makonni ashirin da uku watau watanni biyar kacal da samun cikin ta.

A wannan lamari ya sanya Likitocin da suka karbi haihuwar ta a asibitin San Diego dake kasar Amurka, suka yiwa mahaifiyar ta bakin albishir da cewa jaririyar ta ba za ta wuce fiye da sa'a guda ba a duniya za ta koma ga Mahaliccin ta.

Cikin kudira da Irada ta Mabuwayi Ubangijin Sammai da Kassai, ya sanya Saybie bayan shafe watanni biyar a katarar likitoci su na duban lafiyar ta babu dare babu rana a gadon asibiti, ta koma gida bayan sallama tare da mahaifiyar ta cikin karsashi da koshin lafiya.

KARANTA KUMA: Rayuka 15 sun salwanta yayin wani artabu a gidan yari

Jaririya Saybie ta shafe tsawon watanni biyar a asibitin Mata da kuma jarirai na Sharp Mary Birch dake kasar Amurka bayan da nauyin ta ya kai kimanin kilo 2.5 tare da samun lafiyayyen bugun zuciya kamar yadda wani likitan Yara Dakta Paul Wozniak ya bayar da shaida.

Kwararrun kiwon lafiya sun bayar da shaidar cewa, jariran da aka haifa bayan samun cikin su kasa da makonni ashirin da hudu su kan zo duniya da matsaloli da dama musamman nakasun numfashi, cin abinci, matsalar kwakwalwa da zuciya da kuma barazana ta kamuwa da miyagun cututtuka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel