Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan Boko Haram sun yiwa mutane bakwai yankan rago a Maiduguri

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan Boko Haram sun yiwa mutane bakwai yankan rago a Maiduguri

- An yiwa mutane bakwai yankan rago a wasu kauyuka kusa da garin Maiduguri, a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai

- Rahotanni sun nuna cewa 'yan Boko Haram din sun kai harin ranar Lahadi da daddare

Sama da mutane bakwai ne aka yiwa yankan rago a daren ranar Lahadi, yayin da ake zargin 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari wasu kauyuka dake karkashin mulkin, Bulama Isa da kuma Bulama Mustapha Mallambe.

Duka garuruwa biyun suna yankin yamma da tsohuwar hanyar Gombe, Biu, Damboa da Maiduguri, wadanda suka yi iyaka da sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, wanda yake dauke da dubunnan mutane da suka yi hijira daga Gwoza, Monguno, Nganzai, Damasak da kuma wasu kananan hukumomin da 'yan ta'addar suka kai hari.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan Boko Haram sun yiwa mutane bakwai yankan rago a Maiduguri
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan Boko Haram sun yiwa mutane bakwai yankan rago a Maiduguri
Asali: Facebook

Makonni biyu da suka gabata, abu makamancin haka ya faru a wani kauye mai suna Moramti wanda yake bai fi tafiyar kilomita daya ba zuwa garin Maiduguri, babban birnin jihar.

A cewar wani wanda ya tsira dakyar, wanda ya bayyana sunansa da Kachalla Adam ya ce, "Mutane bakwai aka yiwa yankan rago a garin Bulama Isa da Bulama Mustapha Mallambe kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, yanzu haka ana can ana binne wadanda aka yanka din."

KU KARANTA: Yadda na ceci raina da kyar a mazabata - Sanata

Hakazalika wani mutumi shi ma da ya sha dakyar lokacin kai harin, ya ce kimanin mutane shida ne aka kashe sannan kuma 'yan ta'addar sun sanyawa gidaje da dama wuta, a lokacin da suke kwasar kayan abinci.

A cewar sa, lokacin da 'yan ta'addar suka kai harin babu jami'an tsaro ko kadan a kauyukan.

Duk da cewar an yi kokarin jin ta bakin jami'an tsaron dake yankin amma hakan bai yiwu ba, mun samu rahoton cewa an aika da jami'an tsaro yankin da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, yayin da al'ummar kauyukan suke binne wadanda suka rasa rayukan nasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel